Majalisar Dinkin Duniya ta sanya Saudiyya a jerin kasashen da za ta fitar wadanda ke kashe yara a lokutan yaki, saboda rawar da take takawa a gamayyar da take jagoranta wajen yakin Yemen.
Sanarwar da MDD ta fitar ta ce ayyukan gamayyar kasashen sun jawo mutuwar yara 638 a shekarar 2016, ta kuma zargi gamayyar da kai hare-hare 38 kan makarantu da asibitoci.
Haka kuma MDD ta sanya dakarun gwamnatin Yemen, wadanda gamayyar ke jagoranta da kuma kungiyar Houthi a daftarin jerin wadanda suke kashe yara lokutan yaki.
Sai dai gamayyar kawancen kasashen ta yi watsi da batun cewa tana sane take kai hare-hare kan fararen hula da kuma gine-gine.
An kashe fiye da mutum 8,530, wadanda kashi 60% daga cikinsu fararen hula ne, kuma hare-haren sama sun jikkata mutum 48,800 tun daga watan Maris din 2015, a cewar MDD.
Yakin na Yemen ya kuma bar mutum miliyan 20.7 cikin tsananin bukatar agajin gaggawa, al'amarin da ya jawo tsananin bukatar abinci da ba a taba ganin irin sa ba a duniya
A ko wacce shekara, sakataren MDD na fitar da rahoto kan yara da yake-yake wanda ke dauke da jerin sunaye na wasu bangarori da ake zargi da take hakki.
Daftarin rahoton na baya-bayan nan na cewa: "A Yemen, ayyukan gamayyar kasashen da Saudiyya ke jagoranta ya jawo kashe yara har 638, kuma an samu wannan adadi ne bayan an tabbatar da cewa ita ke da alhakin kai hare-hare 38 a makarantu da asibitoci a shekarar 2016."
Su kuwa kungiyoyin Houthi da na al-Qaeda da dakarun da ke goyon bayan gwamnati wannan ne karo na biyu a jere da ake lissafa su a 'masu wannan laifi.'
Haka kuma rahoton ya nuna karara cewa MDD ta yi amanna gamayyar kasashen 'ta fara daukar matakan da suka dace a lokacin da ake hada daftarin rahoton don tabbatar da bai wa yara kariya."
Wakilin Saudiyya na dindindin a MDD, Abdallah al-Mouallimi, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa ba zai ce komai ba kan rahoton har sai sakataren Majalisar António Guterres, ya amince da shi a hukumance nan gaba cikin wannan watan na Oktoba.
Sai dai a watan Agusta Saudiyya ta ce babu wani tabbaci da zai sa a sanya gamayyar kasashen da take jagoranta a jerin bangarorin da suke kisan yara a lokutan yaki.
Shi ma mai magana da yawun MDD Stephane Dujarric ya ki cewa komai kan daftarin rahoton.
Shugaban kungiyar Save The Children mai fafutukar kwatowa yara hakkokinsu Helle Thorning-Schmidt, ya ce, "Sakataren MDD ya yi abin da ya dace don kwatowa yaran da suke yankunan da ake yaki hakkokinsu.
"Hakan zai sa duk bangarorin da aka sanya a wannan jeri da ma duk wani bangare da ke da hannu a yakin Yemen shiga taitayinsu, da ma kasashen da ke goyon bayansu da ba su makamai."
A bara dai an cire gamayyar kasashen da Saudiyya ke jagoranta daga jerin sunayen da aka fitar na shekarar 2015, duk kuwa da korafin da kungiyar Save The Children ta yi.
Source: BBC Hausa
Title :
MDD Tasa Saudiyya A Kasashe Masu Kisan Yara
Description : Majalisar Dinkin Duniya ta sanya Saudiyya a jerin kasashen da za ta fitar wadanda ke kashe yara a lokutan yaki, saboda rawar da take takawa...
Rating :
5