Wani bincike ya nemi a kara matsa kaimi wajen dakile matsalolin tabin hankali a wajen aiki.
Rahoton wajen aiki mai nagarta ya ce mutane 300,000 da suka dade da larurar tabin hankali yana zama musu tilas su bar aikinsu a ko wacce shekara.
Kuma wannan yana sa Birtaniya tana rasa fam biliyan 97 kimanin naira triliyan 47 a ko wacce shekara.
Mutum uku sun bayyana wa BBC yadda suka hadu da matsalarsu ta tabin hankali a wajen aiki.
Stephanie da Landan ta ce ya kamata a samar da gagarumin sauyi kan yadda ake tunkarar matsalar tabin hakali a wurin aiki.
"A matsayina na wacce take fama da bakin ciki da fargaba, ba zan iya tattauna matsalar tabin hankalina da wadanda suka dauke ni aiki ba.
"Akwai wata al'ada - musamman a cikin ofisoshi - wadda ke ganin wannan a matsayin wata alama ta rauni ko kuma rashin iya tafiyar da aikinsu."
Stephanie ta daura laifin ne kan al'adar dadewa ana aiki kullum, inda manajoji ke sa ma'aikata su ji sun yi laifi idan suka dauki hutun lokacin cin abinci.
"Akwai bukatar gagarumin sauyi kan yadda ake tunkarar lafiyar hankali," wadda ta ce, "ba za a iya magance ta da horaswa kadan a wajen aiki ba."
Daisy daga Taunton ta fuskanci yanayi biyu na tunkarar matsalar lafiyar hankali a wajen aiki.
Daisy ta yi aiki tare da wata hukuma, amman ta ce: "Ina ganin suna neman uzurin da za su yi amfani da shi domin su kore ni.
"Na bar aiki domin ban gamsu da wurin aikin da kuma rashin tallafi ba."
"Sauya wurin aiki daga ma'aikatar gwamnati zuwa ta masu zaman kansu ya bude mini ido.
"Na gaya wa masu sabon wurin aikina gaskiya game da matsalolin da nake da su game da lafiyar hankalina, kuma martanin da suka fara mayarwa shi ne, 'ba matsala ba ce'.
"Martanin da suka mayar din wata halayya ce wadda ta ba ni matukar mamaki."
A lokacin da ta samu koma baya a lafiyar hankalinta, ta samu tallafi a kan lokaci: "Wadanda suka dauke ni aiki sun ba ni damar ganawa da wani likitan hankali mai zaman kansa domin ya taimaka musu wajen kara fahimtar halin da nake ciki da kuma samun wani bincike mai zaman kansa.
"Daga baya aka gane cewa ina fama da matsalar saurin sauya halayya da yadda nake ganin kaina da kuma yadda nake aiki wadda ake ce wa Borderline Personality Disorder a Ingilishi, tare da matsalar damuwar bayan shan wahala da nake da ita da damuwa mai tsanani da kuma fargaba.
"Taimakon da wadanda suka dauke ni aiki suka ba ni ya ceci rayuwata".
Lorna daga Ballymena ta bar aikinta sabida matsalolin lafiyar hankali bayan haihuwarta ta uku a shekarar 2006.
Ta gano cewa tsayawa tsayin daka shi ne mataki na farko na warkewa daga matsalar.
"Tsarin kiwon lafiyan ya taimaka mini," in ji ta. "Na yi sa'a sosai na samun taimako cikin gaggawa game da halayya kuma likitana ya lura da cigaban da nake samu a warkewa.
"Amman ni ne na yi tambaya kan ko zan iya daina karbar magani a karkashin kulawa".
Lorna ta kuma koma aikin 'yan wasu lokuta, lamarin da ya rage iya matsin da take samu.
A yanzu haka tana aikin kwana biyar ne kuma tana amfani da kayayyakin aiki tare da mayar da hankali da wani nau'in magani da kuma rubutu wa mujalla domin tattabar da lafiyar hankalinta.
"Har yanzu ina da ranaku da nake jin dadi da kuma ranakun da ba na jin dadi, amman a yanzu na san yadda zan gane yadda nake ji.
"In akwai wani abu da zan iya sauyawa, zan dauki mataki. In kuma ba haka ba - zan rungumi kaddara, warware matsalar sannan in cigaba da rayuwa".
Source: BBC Hausa
Title :
Matsalar Tabin Hankali Nasa Asarar Naira Triliyan 47
Description : Wani bincike ya nemi a kara matsa kaimi wajen dakile matsalolin tabin hankali a wajen aiki. Rahoton wajen aiki mai nagarta ya ce mutane 300...
Rating :
5