Wasu da iyalansu ke hannun mayakan Boko Haram na cigaba da bayyana halin damuwar da suke ciki, a dai dai lokacin da hukumomin Najeria ke ikirarin samun nasara a yakin da suke yi da kungiyar Boko Haram.
Editan BBC na Abuja, Naziru Mikailu ya yi kicibis da wani mutumin garin Bama da ke jihar Borno, wanda yanzu yake Abuja, kuma wanda mayakan Boko Haram suka sace matarsa da 'ya'yansa biyar, shekara hudu da suka gabata.
Ya dai nemi sakaya sunansa saboda mas'alar tsaro.
Ya fara da bayyana makasudin dalilin barin gidansa da garinsa a lokacin da rikicin Boko Haram ya isa garin na Bama:
"A da muna cikin garin Bama ne. To, da abin ya dau wuta, sai muka yi gudun hijira zuwa Kamaru ni da matana biyu da 'ya'yana goma".
Ya ce daga baya ya dawo gida daga Kamaru, kuma ya aika wa iyalan nasa kudi domin su dawo.
"Daya ta sami fitowa daga Kamarun zuwa Bama, amma dayar mayakan sun riketa da 'ya'yanta biyar", in ji mutumin.
Ya ce: "Zai kai shekara uku zuwa hudu da faruwar wannan abun. Sam ban sake jin labarinsu ba, kuma ban san inda suke ba".
Ya ce saboda matsalar ta yaki da Boko Haram, ya kasa komawa ya nemo iyalin nasa a wancan lokacin.
"Ina da niyyar in tafi in duba su, amma ba halin tafiya. Ba hanyar babu halin tafiya".
"Ni da kaina ina kwana biyu ko uku bana iya barci saboda zulumi, kuma idan na tuna da su wani lokaci ba na iya cin abinci ma."
Ya ce har yanzu bai sanar da sauran 'ya'yansa cewa sauran 'yan uwan nasu na hannun mayakan Boko Haram ba.
"Ina gaya musu 'yan uwansu ba su sami tahowa ba, suna can a Kamaru. Idan na sami kudi zan aika musu domin su dawo."
Ya sanar da BBC cewa duk da halin da yake ciki, bai sanar da hukumomi cewa mayakan Boko Haram na rike da maarsa daya tare da 'ya'ya biyar ba, amma yana da karfin zuciyar cewa iyalinsa suna nan raye, kuma wata rana za su hadu.
Source: BBC Hausa
Title :
Matata Da 'Ya'yana 5 Na Hanun Boko Haram
Description : Wasu da iyalansu ke hannun mayakan Boko Haram na cigaba da bayyana halin damuwar da suke ciki, a dai dai lokacin da hukumomin Najeria ke iki...
Rating :
5