A ranar Talata ne majalisar dokokin jihar Sokoto ta dakatar da wasu ‘yan majalisan ta guda biyu.
Majalisar ta dakatar da Sani Yakubu APC da Malami Galadanchi APC dalilin aikata rashin da’a a zauren majalisar da suka yi.
Kafin majalisar ta dakatar da su, sai da ta kafa wata kwamiti don ta gudanar da bincike kan halayen ‘yan majalisan wanda lokacin ya zo daidai majalisar tana tsige mataimakin kakakinta Kabiru Ibrahim.
Majalisar ta dakatar da Sani Yakubu na tsawon kwanaki 40, Malami Galadanchi na tsawon kwanaki 30 sannan ta umurce su da su rubuto wasikar neman gafara majalisar kan rashin da’an da suka aikata a zauren majalisar.
Source: Premium Hausa
Title :
Majalisan Dokokin Jihar Sokoto Ta Dakatar Da 'Yan Majalisu Biyu
Description : A ranar Talata ne majalisar dokokin jihar Sokoto ta dakatar da wasu ‘yan majalisan ta guda biyu. Majalisar ta dakatar da Sani Yakubu APC da...
Rating :
5