'Yan Majalisar dattawan Najeriya da ta wakilai za su gudanar da bincike kan yadda aka dawo da tsohon shugaban kwamitin yin garambawul ga tsarin fanshon kasar, AbdulRasheed Maina bakin aiki.
'Yan Majalisun dokokin dai sun zartar da kudirin ne sakamakon ce-ce-kucen da ya barke a kasar bayan mayar da Maina bakin aiki a matsayin darekta a ma'aikatar cikin gida.
Da suke tafka muhawara ranar Talata, wasu 'yan Majalisar dattawa sun bayyana takaicinsu kan yadda shugaban kasar ke shelar yaki da cin hanci da rashawa sabanin haka a tsakanin wasu mukarrabansa.
Majalisar dattawa ta umurci kwamitocinta da suka hada da na harkokin cikin gida da kwamitin shari'a da kuma kwamitin yaki da cin hanci da rashawa da su gudanar da cikakken bincike kan lamarin.
Su ma 'yan Majalisar wakilai sun kafa wani kwamiti na musamman don binciken yadda aka yi AbdulRasheed Maina ya koma bakin aiki.
Majalisar wakilan ta bukaci hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC da ta gaggauta kama AbdulRasheed Maina domin ya fuskanci shari'a.
'Yan Majalisar wakilan sun kuma sha alwashin ba da shawarar hukunta duk wani da aka samu da hannu a lamarin.
A ranar Litinin ne Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kori AbdulRasheed Maina, daga sabon mukamin mukaddashin darakta a ma'aikatar harkokin cikin gida.
Source: BBC Hausa
Title :
Majalisa Zata Binciki Batun Abdulrasheed Maina
Description : 'Yan Majalisar dattawan Najeriya da ta wakilai za su gudanar da bincike kan yadda aka dawo da tsohon shugaban kwamitin yin garambawul ga...
Rating :
5