A kalla yara 'yan dugui-dugui hudu ne da malama daya suka rasa ransu a Brazil, bayan da wani maigadi ya cinna wuta a wata makarantar kananan yara.
Mutumin sai da ya watsa wa yaran da ke makarantar man fetur, sannan shi ma ya zuba wa kansa kafin ya kunna wutar.
Bayan yaran da malamar shi ma maigadin ya mutu sakamakon kunar da ya samu.
Har yanzu ba a kai ga gano dalilin mutumin na aikata wannan ta'asa ba, amma kuma wasu kafafen watsa labaran kasar sun ce, an kori maigadin ne daga aiki bayan ya dawo daga hutunsa na shekara saboda yana fama da wata rashin lafiya.
Wasu hotunan bidiyo da aka dauka sun nuna yanayin wurin da lamarin ya faru, inda iyayen yaran da ke makarantar ke ta kururuwa bayan da suka samu labarin afkuwar lamarin.
Yanzu haka dai akwai yara wadanda shekarunsu ba su wuce hudu zuwa biyar ba su 25 da ke kwance a asibiti saboda kuna da raunukan da suka samu.
Shugaban kasar Michel Temer, ya bayyana a shafinsa na twitter cewa, yana matukar jimami a kan wannan lamari da ya afku, inda ya mika sakon jajensa ga iyalan wadanda abin ya rutsa da su.
Sannan ya ce, a matsayinsa na uba, yana jin irin ciwon da iyayen yaran da wannan iftila'i ya shafa ke ji a zuciyarsa.
Source: BBC Hausa
Title :
Maigadi Ya Kona Kansa Da 'Yan Makaranta
Description : A kalla yara 'yan dugui-dugui hudu ne da malama daya suka rasa ransu a Brazil, bayan da wani maigadi ya cinna wuta a wata makarantar kan...
Rating :
5