Mummunar annoba ta yi wa al'umma dabaibayi.
Bazuwarta ya karade ko'ina a duniyarmu mai gagarumin ci gaban birane cike da al'umma da jiragen sama masu kai-kawo a sararin samaniya, sai dai mun gaza shawo kan al'amuran tsawon lokaci.
Bunkasar harkokin rayuwar al'umma ya tarwatse, idan dumbin mutane suka mutu sai ka ji kamar ka zautu, amma saboda wasu makarai na jiki sai ka shawo kan matsanancin zazzabi, ka farka a gida mai sanyi, babu wutar lantarki ba ruwan famfo ko gas din hura wutar dumama ruwa ko girki.
Tituna za su yi tsit babu kowa, babu jirgin sama da ke shawagi a sama.
Kai kadai ka tsira a wannan rikirkitaccen al'amari na karshe.
Wadannan su ne bayanan da aka yi ta hakaito mana daga cikin littattafai, wadanda suka hada da "Can ticle for Leibowitz ko The Road," har ma da wasan kwamfuta na baya-bayan nan irinsu "the Last of Us da fina-finai kamar Am Legend ko Mad Max.
Daukacin wadannan labaran suna nuni da fahimtar masu ra'ayin mutanen da ke sanya warki, su yi ta gararamba a daji.
Ko mene ne hakikanin gaskiyar wadannan al'amura?
Kirkirarren labari game da tashin duniya nuni ne ga fahimtar wadanda ba sa sanya tufafi illa warki.
Idan ka samu kanka a matsayin wanda ya tsira daga masifar da ta tarwatsa duniya ta share mafi yawan mutane daga doron kasa. Ko me za ka iya yi?
Irin wannan ne muhimmin ilimin da kake bukata don tsira, har ka kara ci gaba da bunkasa?
A nan ne gwanintakarka za ta kai makura.
Mutuwar yawa kaka! Tabbas za mu samu damar ci gaba ne ta hanyar bibiyar tarihi, inda muka gina duniya mai ci gaban zamani a matakin farko ta hanyar aikin hadin gwiwar zamantakewar halittu, tuni da ma al'umma ta ginu kan tsarin zamantakewa.
Duk da cewa za a samu yamutsi bayan wargajewa, mutane za kuma su sake zama cikin tsarin al'ummomi ba da dadewa ba.
Tambayar dai ita ce saura da me..?
Wadanne al'amura ya kamata ka ba fifiko, kuma mene ne ya kamata al'ummarka ta kara kaimi wajen ganin ta farfado da shi bayan shekaru?
Wannan shi ne daya daga cikin mai yiwuwa a jerin al'amura.
Kwanakin farko
Da zarar mutane sun daina sa ido da gyara tashoshin samar da makamashi, sadarwa za ta gaza cikin sauri.
Sai dai a koma laluben faifan zuko makamashin rana ko amfani da jannareto daga wani gini, ta yadda za ka samu wutar lantarki na wucin gadi.
Intanet za ta shafe nan da nan, da zarar rumbun sakonnin kwamfyutocinsu ya daina aika sakwanni, da zarar man fetur din da ke cikin jannareto ya kare, don haka kada ka dauka za ka ci gaba da dogara da Wikipedia wajen samun ilimi.
Sai dai wannan ba yana nufin wayarka ta alfarma za ta zama fanko ba ne.
Manuniyar hanyar cikinta na amfani da ma'aunin maganadisu, ta yadda za ka ci gaba da gefa ne hanyarka lokacin da kake tafiya, kuma a gaskiya taswirar da ke kan wayar za ta ci gaba da taimaka maka wajen gane inda ka dosa (GPS).
Manunin taswirar tauraron dan Adam zai ci gaba da aiki na wasu makonni bayan rushewar al'amura, amma bayan wata shida aikin da yake yi daidai zai wargaje ya daina amfani kwata-kwata.
Abubuwan da za ka fifita su ne ka tabbatar ka tara ruwa da abincin gwangwani da managartan suturun fita waje.
Makonnin farko
A makonnin farko ta yiwu ka hadu da wasu mutane kalilan da suka tsira.
Ka yi taka-tsantsan wajen hulda da baki har sai ka hadu da wadanda ka aminta da su, wadanda za ku yi taimakekeniyar ba wa juna kariya, kuma zai yi matukar taimakawa wajen hada karfi a fafutukar tara abincin da kuke bukata.
A yanzu yankin birnin da ka fara harkoki ya fara rashin dadi.
Warin gawawwakin da suka rube ya cika iska, ga karnukan da ke jin yunwa sun yi gungu.
Ko ta wane halin, birni na zamani ya cika da kirkirarrun abubuwa, wadanda suka dogara kan tsarin ci gaban rayuwar da ta samar da su.
Rashin lantarkin da ke motsa matakalar bene da haskaka hanya, tsaftataccen ruwa zai zamo gurbatacce, kasa na zirga-zirga, jirgi zai zama tundurki, don haka rayuwa za ta yi maka sauki a karkara.
Gidan gona na al'ada da murhun wuta, inda girki zai yiwu cikin dadi bayan rushewar kayan amfani na zamani.
Za ka iya bincike tarin sharar sassan birane don tara abinci ko kayan amfani, a daidai lokacin da kake kokarin sake koyon yadda za ka kirkiro abubuwa da kanka.
Watannin farko
Abin da zai fi damunka shi ne yadda za ka samu tsaftataccen ruwan sha, ka kuma kauce wa cututtukan da ke bazuwa a cikin ruwa, wadanda suka cutar da mutane dubban shekaru.
Tafasawa hanya ce ta kashe kwayoyin cuta a ruwa, amma tana bukatar dumbin makamashi daga burbushin abubuwa da suka rage, amma wata rana dole sai ka yi amfani da dabarun sarrafa sinadarai don tabbatar da cewa ruwan da kake kai wa bakinka bai halaka ka ba.
Za a iya tsaftace ruwa daga sinadaran kwayoyin cuta da ke kara-kaina a dakin girki ko kududdufan ninkaya da za ka zuba sinadarin Chlorine (Sodium hypochlorite and Calcium hypochlorite) sai a narkar da shi yadda zai kashe kwayoyin cuta, amma babu gubar da za ta cutar da kai.
A nan kana amfani da kimiyyar sinadarai wajen sarrafa chlorine, don inganta ruwan famfon da muke sha a yau, wanda zai zamo tarihi, tun da irin wannan ci gaban a fannin tsafta da kula da lafiyar al'umma ya taimaka mana wajen zama a biranen da ke kwasar dumbin mutane a cakude.
Har sai ka samu dabarar sarrafa chlorine ta kashin kanka, wata karamar fasahar tsaftace ruwa da ake amfani da makamashin rana.
Irin wannan dabarar Hukumar Lafiya ta Duniya na koyar da ita a kasashe masu tasowa, kuma kawai cika robar ruwa ake yi da ruwan ake ganin ya gurbata a bar shi cikin rana tsawon kwana daya ko biyu.
Makamashin hasken rana zai ratsa cikin robar ruwan ya kashe kwayoyin cutar.
Wanke hannayenka ma yana da matukar alfanu wajen hana yaduwar cuta.
Za a iya yin sabulu ta hanyar tatso kitsen dabba ko man tsirrai; ta hanyar tafasa sinadarin alkaline.
Alkaline na da matukar muhimmanci cikin jerin sinadarai a daukacin tarihi, kuma za a iya kwakwulo shi daga muhallinka.
Kanwa (Potassium Carbonate) za a iya ciro ta, ta hanyar zuba ruwa a cikin tokar itacen girki, sannnan tokar soda daga burbushin tsirran teku da aka kona ko gishirin tsirran da ke gabar ruwa irinsu samphire ko saltwart.
Tattara tsirran teku don samar da soda babbar harka ce a gabar Tekun Atlantic ta kasar Scotland da Ireland tsawon karnoni.
Gobe za mu wallafa muku ci gaban wannan makala mai taken: 'Yadda za a tunkari karshen duniya.'
Source: BBC Hausa