An fayyace kungiyar da Real Madrid ya kamata ta kara da ita a gasar cin kofin duniya ta zakarun nahiyoyi ta bana.
A jadawalin da aka fitar a Abu Dhabi, Real mai rike da kofin za ta yi wasan daf da karshe a ranar 13 ga watan Disambar 2017.
Madrid din za ta fafata tsakaninta da Al-Jazira mai rike da kofin hadaddiyar daulal Larabawa ko kuma Auckland City zakarar nahiyar Oceania ko wacce ta ci kofin Asia.
Aljazira da Aucland City za su fara karawa a tsakaninsu, kuma duk wacce ta samu nasara ta fafata da Real Madrid.
Ga yadda aka raba jadawalin:
Zagayen farko:
Ranar 6 ga watan Disamba Al-Jazira da Auckland City
Zagaye na biyu: Ranar 9 ga watan Disamba
Pachuca da Zakaran Afirka
Al-Jazira ko kuma Auckland City da zakaran Asia
Wasannin daf da karshe:
Ranar 12 ga watan Disamba Zakaran Conmebol da wacce ta yi nasara tsakanin Pachuca da Zakarar Afirka
Ranar 13 ga watan Disamba Al-Jazira ko Auckland City ko zararar Asia da Real Madrid
Ranar 16 ga watan Disamba Za a buga neman mataki na uku da na hudu
Ranar 16 ga watan Disamba Wasan karshe Final
Source: BBC Hausa
Title :
Madrid Zasu Kare Kofinta A Duniya
Description : An fayyace kungiyar da Real Madrid ya kamata ta kara da ita a gasar cin kofin duniya ta zakarun nahiyoyi ta bana. A jadawalin da aka fitar ...
Rating :
5