Mai rike da kofin La Liga na Spaniya, Real Madrid ta yi rashin nasara a gidan Girona da ci 2-1 a wasan mako na 10 da suka kara a ranar Lahadi.
Real ce ta fara cin kwallo ta hannun Isco a minti na 12 da fara tamaula, kuma haka aka je hutun rabin lokaci.
Bayan da aka dawo ne Girona ta farke kwallo ta hannun Cristhian Stuani daga baya kuma Portu ya kara ta biyu, tun farko dan wasan da Pablo Maffeo sun buga kwallo ta bugi turke.
Wannan ne karo na biyu da aka ci Real Madrid a La Liga, bayan da ta yi rashin nasara da ci daya mai ban haushi a hannun Real Betis a Barnebeu a ranar 20 ga watan Satumbar 2017.
Da wannan sakamakon Madrid tana ta uku a kan teburi da maki 20, inda Barcelona wacce take ta daya ta ba ta tazarar maki takwas.
Source: BBC Hausa
Title :
Madrid Tasha Kashi A Hanun Girona
Description : Mai rike da kofin La Liga na Spaniya, Real Madrid ta yi rashin nasara a gidan Girona da ci 2-1 a wasan mako na 10 da suka kara a ranar Lahad...
Rating :
5