Kimanin mutum miliyan 5.4 ne dai maciji kan sara a duk shekara a duniya, adadin wadanda kan rasa rayukansu kuma ya kama daga 81,000 zuwa 130,000, kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya(WHO) ta bayyana.
Akwai kuma mutane da dama da ke rasa gabbansu da kuma nakasa sanadiyyar saran macijizai. Najeriya dai na daya daga cikin kasashen da macizai ke barna sosai.
BBC ta ziyarci yankin Kaltungo da ke jihar Gombe, daya daga cikin wuraren da matsalar ta fi kamari a Najeriya.
Al'ummomi da dama a kasar dai na rayuwa ne kullum cikin fargaba saboda da matsalar saran majici, musamman yanzu lokaci damina zuwa kaka.
Manoma da kuma kananan yara ne matsalar ta fi shafa.
Da dama daga cikinsu a kan kai su asibitin jinyar sarar maciji ne da ke garin Kaltungo, daya daga cikin cibiyoyi kalilan na musamman domin jinyar sarar maciji da ake da su a kasar.
An kawo wata yarinya mai suna Haraja, mai shekaa 16 wannan asibiti a sume, kwana hudu bayan da maciji ya sare ta.
Cikin kasa da sa'o'i 24 daga bisani kuma budurwar ta rasu.
Daga nan ne sai aka yi jana'izarta a wata makabarta da ke kusa da asibitin.
Kawunta mai suna Abubakar Muhammmad, ya shaida wa BBC cewa rashin kudin zuwa asibiti ne ya sanya jinkirin kai ta cibiyar ta sarar maciji.
Kububuwa ce ta fi kai wa mutanen wannan yankin farmaki, inda take sararsu ba babba, ba yaro.
Wata dattijuwa mai suna Misis Trihana Yayinus, wadda take kwance a gadon asibitin, ta shaida wa BBC cewa ta sha azaba a wajen kubuwa domin kwananta uku a sume bayan ta sare ta a gona.
Wata babbar matsalar dai ita ce yadda wadanda macijin kan sara ba sa samun magani yadda ya kamata.
Ba a yin maganin a Najeriya amma a kan shigo da maganin ne daga kasar Birtaniya da kuma yankin kudancin Amurka bayan an kai samfurin macizan da kuma dafin daga Najeriya.
Wasu lokuta dai magani kan kare karkaf a cibiyar ta Kaltungo, amma a kullum marasa lafiya sai kwarara suke yi domin neman maganin.
Ko baya ga wadannan alkaluma, akwai kuma wasu dubban a wasu yankuna na Najeriya wadanda macijin kan sara a duk shekara.
Kuma masana na cewa samar da magani a kan kari da kuma kai duk wanda maciji ya sara asibiti da wuri za su taimaka matuka wajen rage yawan mace-macen.
Hakan kuma zai kawo karshen wahalar da daya daga cikin halittu mafiya hadari a duniya ke haddasawa.
Source: BBC Hausa
Title :
Macizai Nasaran Sama Da Mutum Miliyan Biyar A Shekara-WHO
Description : Kimanin mutum miliyan 5.4 ne dai maciji kan sara a duk shekara a duniya, adadin wadanda kan rasa rayukansu kuma ya kama daga 81,000 zuwa 130...
Rating :
5