Kocin Manchester United, Jose Mourinho ya ce ya kamata Romelu Lukaku ya zama shafaffe da mai a wajen magoya bayan kungiyar ba wai sukarsa ba.
Lukaku wanda ya koma United a bana kan kudi fam miliyan 75 daga Everton ya ci mata kwallo 11 a wasa 10 da ya yi, amma yanzu ya buga wasa biyar bai ci kwallo ba.
Mourinho ya ce dan wasan yana yi wa kungiyar kokari, kuma ba wai kawai cin kwallo ne aikinsa ba.
Kocin ya kara da cewar Lukaku shafaffe da mai ne a wajensa ya kamata ya zama hakan a wajen magoya baya, ya kuma kamata su dunga martaba shi.
United za ta karbi bakuncin Benfica a ranar Talata a gasar cin kofin Zakarun Turai.
Source: BBC Hausa
Title :
Lukaku Shafaffe Da Mai Ne-Mourinho
Description : Kocin Manchester United, Jose Mourinho ya ce ya kamata Romelu Lukaku ya zama shafaffe da mai a wajen magoya bayan kungiyar ba wai sukarsa ba...
Rating :
5