Liverpool ta ci Maribo 7-0 a gasar cin kofin Zakarun Turai da suka fafata a wasan cikin rukuni na biyar.
Wannan ne kwallaye da yawa da kungiyar ta ci a tarihin gasar tun bayan shekara 10, kuma hakan ya sa tana ta daya a kan teburi tare da Spartak Moscow da maki iri daya.
Fermino da Mohamed Salah kowanne ya ci kwallo bibiyu sai Coutinho da Oxlade-Chamberlain da kuma Alexander-Arnold da kowanne ya ci dai-dai.
Liverpool ta taba cin Besiktas 8-0 a gasar cin kofin Zakarun Turai a ranar 6 ga watan Nuwamba.
Daya wasan rukuni na biyar din Spartak Moscow ce ta doke Sevilla 5-1.
Ga sakamakon wasu wasannin da aka yi:
Feyenoord Rotterdam 1 : 2 Shakhtar DonetskApoel Nicosia 1 : 1 BV Borussia DortmundReal Madrid CF 1 : 1 TottenhamAS Monaco 1 : 2 BesiktasRB Leipzig 3 : 2 FC PortoSpartak Moscow 5 : 1 SevillaManchester City 2 : 1 SSC Napoli - Italy
Source: BBC Hausa
Title :
Liverpool Tayi Wa Maribo Ruwan Kwallaye
Description : Liverpool ta ci Maribo 7-0 a gasar cin kofin Zakarun Turai da suka fafata a wasan cikin rukuni na biyar. Wannan ne kwallaye da yawa da kung...
Rating :
5