An shiga mataki na gaba a gasar rubutun kagaggun labarai ta mata ta BBC Hausa, bayan da aka fitar da jerin labaran da za a zabi wanda ya yi zarra.
A ranar 30 ga watan Satumba ne dai aka rufe karbar labarai daga masu sha'awar shiga gasar, sannan wasu kwararru suka shiga aikin tantance labaran a bisa ma'aunin da aka shimfida ka'idojinta.
Kwararrun dai sun duba labarai kusan 340, suka fitar da guda 60, wadanda daga cikinsu aka zabo 25 din da suka kai mataki na gaba (duba teburin da ke kasa).
Labarai 25 da suka kai mataki na gaba1.Adikon Zamani2.A Hanyar Talla3.Almajiri4.Amanar Aure5.Bai Kai Zuci Ba6.Direban Hajiya7.Dubu ta Cika8.Garin Neman Gira9.Hangen Dala10.Hattara dai Iyaye11.Karfin Hali12.Labarin Ladidi13.Lauren Tirmi14.Mafarkin Uwa15.Matsalarmu16.Saki Kowa17.Sana'a Sa'a18.Sanadi19.Sanadin Fyade20.Sanadiyya21.Son Zuciya Bacinta22.Tsalle Daya23.Yau24.'Ya'ya Mata25.Zawarcina
Ma'aunan da aka yi amfani da su don tantance 25 din sun hada da abin da zai rike hankalin mai karatu; da kyawun rubutu—ma'ana, rubuta haruffa yadda ya kamata, da amfani da wakafi ko aya yadda ya dace.
Har ila yau, an duba amfani da kalmomin da suka dace; da kuma iya kirkira da tsara labari da bayar da shi ta yadda komai zai gudana a inda ya dace kuma a lokacin da ya dace tun daga farko har karshe.
Sauran ma'aunan su ne iya kirkirar jarumai wadanda ke da dabi'ar da ta dace da rawar da suke takawa a labarin da muryoyin da suka kamace su.
Haka zalika da hirarrakin da suka dace da rayuwarsu; da sakon da labarin ke son isarwa; da kuma yiwuwar burge masu karatu ko sauraron labarin.
Nan da 'yan kwanaki masu zuwa ne alkalan gasar za su duba wadannan labarai guda 25 su fitar da wanda ya ciri tuta, da na biyu, da kuma wanda ya yi na uku.
A watan gobe ne ake sa ran karrama marubuta labarai ukun da suka yi nasara a birnin Abuja.
Za a bai wa wacce ta yi ta daya kyautar $2,000 da lambar yabo, wadda ta zo ta biyu kuma za a ba ta $1,000 da lambar yabo, yayin da ta uku za ta karbi kyautar $500 da lambar yabo.
A bara ne dai sashen Hausa na BBC ya kaddamar da gasar ta Hikayata da nufin bai wa mata damar bayyana abin da ke damunsu a rayuwa.
Source: BBC Hausa
Title :
Labarai 25 Da Aka Tantance Na Gasar Hikayata Na 2017
Description : An shiga mataki na gaba a gasar rubutun kagaggun labarai ta mata ta BBC Hausa, bayan da aka fitar da jerin labaran da za a zabi wanda ya yi ...
Rating :
5