Wata kungiya a Birtaniya ta yi gargadin cewa jakuna na fuskantar mafi girman hadarin bacewa daga doron kasa, sakamakon yadda ake matukar bukatar fatarsa da sauran wasu abubuwa na jikinsa a China, inda yanzu ake kashe miliyoyin jakuna.
Kungiyar mai suna ''The Donkey Sanctuary'' da ke Devon, tana gargadin cewa yadda ake amfani da fatar jaki wajen yin maganin gargajiya hakan na matukar shafar iyalan da suka dogara da dabbar wajen safarar kaya da kuma noma, musamman a Afirka.
A yanzu dai akwai mayankar jakuna har guda uku a babban birnin Kenya, Nairobi, domin samar da fatun da ake bukata kamar yadda wakilin BBC na Afirka Alastair Leithead ya gano.
A fadin kasashen Afirka kusan a ko ina ana bukatar jaki. Yawan jakunan da ake da su yanzu a China ya karu matuka, jaki dai dabba ce da ba ta da saurin yaduwa, kuma a nan Kenya farashin dabbatar ya linka biyu a cikin shekara biyu, yayin da 'yan kasuwa ke kokarin samar da fatu da sauran sassan jakin da ake bukata.
Ana dafa fatar jaki ne dai domin samar da wani sinadari (gelitine) a hada wani abinci mai kara lafiya wanda aka yi amanna cewa yana jinkirta tsufa da kuma maganin cutar daji.
Wasu kuma na ganin cewa sinadarin ya kan taimaka wajen rage matsalar da mata ke fuskanta idan suka kai munzalin da jinin haila ya dauke musu.
Haka kuma ana amfani da fatar wajen magance matsalar barci.
Kasuwancin fatar jakunan na kawo miliyoyin daloli, tana kuma da amfani mai tarin yawa ga kasar China inda ake hada magungunan da ita.
Kungiyar kare hakkin jakin, wadda ta dade tana gudanar da bincike kan kashe jakunan, ta ce a yanzu ana kashe miliyoyin dabbar, kuma da dama ana wahalar da su.
Jaki yana da muhimmanci da darajar gaske musamman ga iyalai talakawa a Afirka, inda suke amfani da shi a harkar sufuri, da sauran fannoni na rayuwa, to amma a yanzu sakamakon tsadar da ya yi, sai ake satar shi.
Kuma abin takaici ya kasance yana da tsadar da idan an sace wa iyali wasu ba za su iya sayen wani ba.
A Kenya yanzu akwai mayanka har guda uku, wadanda ba naman dabbar da ake sarrafawa sai na jaki kawai.
To amma yanzu akwai kasashe kusan gommai da ko dai suka hana sayar da jaki ko kuma suka takaita sayar da shi, saboda tasirin da kasuwancin nasa ke yi ga rayuwar jama'a musamman talakawa, da kuma hadarin karewarsa a duniya.
Source:BBC Hausa
Title :
Kunsan Yadda Ake Amfani Da Fatan Jaki Wajen Maganin Tsufa?
Description : Wata kungiya a Birtaniya ta yi gargadin cewa jakuna na fuskantar mafi girman hadarin bacewa daga doron kasa, sakamakon yadda ake matukar buk...
Rating :
5