Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta samu nasara kan Brighton da ci 2-0 a wasan da suka buga a gasar firimiya ranar Lahadi.
Nasarar da kulob din ya samu ta zo daidai da ranar da kocin kungiyar Arsene Wenger yake cika shekara 21 da fara jagorancinsa.
Har ila yau nasarar ta sa kungiyar a mataki na biyar a teburin gasar firimiya.
A sauran wasannin da aka fafata a gasar ranar Lahadi, Everton ta yi rashin nasara a hannun Burnley.
Yayin da Newcastlee ta buga kunnen doki (1-1) da Liverpool.
Source: BBC Hausa
Title :
Kungiyar Arsenal Ta Lallasa Brighton
Description : Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta samu nasara kan Brighton da ci 2-0 a wasan da suka buga a gasar firimiya ranar Lahadi. Nasarar da kulob...
Rating :
5