Wasu 'yan harin kunar bakin wake guda biyu sun kai hari Garejin Muna cikin Maiduguri babban birnin jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya.
Rahotannin farko-farko sun bayyana fargabar mutuwar mutane da dama.
Harin na maraicen ranar Lahadi, ya zo ne bayan an samu lafawar hare-haren 'yan ta-da-kayar-baya a yankin.
A karshen watan Yuli ne, Mukaddashin Shugaban kasar Yemi Osinbajo ya umarci manyan hafsoshin tsaron Najeriya su koma birnin Maiduguri da zama.
Manyan hafsoshin tsaron sun tare a can din ne bayan wani mummunan hari da kungiyar Boko Haram ta kai wanda ya yi sanadin mutuwar fiye da mutum 40.
Muna tafe da karin bayani, nan gaba kadan!
Source: BBC Hausa
Title :
'Yan Kunar Bakin Wake Sun Far Wa Maiduguri
Description : Wasu 'yan harin kunar bakin wake guda biyu sun kai hari Garejin Muna cikin Maiduguri babban birnin jihar Borno a arewa maso gabashin Naj...
Rating :
5