Daya daga cikin limaman addinin musulunci na Asibitin kula da mutanen da maciji ya sara a cikin jihar Gomben Najeriya, Malam Tukur Tela ya ce kusan kullum sai sun jagoranci sallar jana'iza ta mutanen da maciji ya yi ajalinsu.
"Wannan wuri, kullum za mu yi jana'izar mutum biyu zuwa uku, kuma duk cizon maciji ne."
Ya ce sai a dauko mutum sakamakon cizon maciji a kawo shi zuwa asibiti amma a tarar babu magani.
"Idan an zo babu magani, sai a ce mutum sai ya tashi ya shiga mota zuwa Gombe, Ka je tasha ka zauna jiran mota tsawon sa'a biyu ko uku.
Ka je, ka sayo maganin, ka dawo tasha a Gombe, sai ka yi zama na sa'a biyu ko uku, kafin ka iso Kaltungo, majinyacinka ko yana da rai, ya jigata."
A cewarsa: "Idan larurar ta same ka, ba ka da kudi, kana ji kana gani, dan'uwanka zai rasu".
Ya ce a shekarun baya da ake samun magani a cibiyar, ba a cika samun wannan mace-mace ba.
Wakilin BBC da ya ziyarci yankin Kaltungo, Ishaq Khalid ya ce wata babbar matsalar ita ce yadda mutanen da maciji ya sara ba sa samun magani yadda ya kamata, baya ga talauci.
Kudin maganin yakan kai fiye da Naira dubu 30, kuma idan mutum bai dace ba, sai an yi masa magani sau biyu ko uku, abin da ke nufin za a iya kashe fiye da Naira dubu 100 wajen jinya, in ji shi.
Shugaban Cibiyar kula da mutanen da maciji ya sara, Dr. Abubakar Balla ya ce kowacce rana suna samun akalla mutum 12 da akan kai su bayan maciji ya sare su.
Likitan ya alakanta rashin magani a cibiyar da kuma zuwa asibiti a makare a matsayin wasu daga cikin sabbuban da kan janyo mutuwar mutanen da maciji ya sara.
Dr. Abubakar Balla ya ce shan magungunan gargajiya na kara ta'azzara matsalar, abin da zai kai ga cire yatsa ko a yanke kafa ko hannu don kuwa wasu kan tsattsarga sashen da macijin ya sara.
Shi ma wani manomi a yanki, Maina Alhassan ya ce suna cikin matukar fargaba da taka-tsantsan duk lokacin da suka je gona.
"Dole ne mu zamto cikin fargaba domin yau idan muka daina noma to babu abin da za mu ci. Ya zamto tilas mu fita mu yi noma, kuma idan maciji ya sari wani, to mukan samu matsala da asibiti."
Ya ce matsalar magani! Akalla sai ka tanadi sama da Naira dubu 100, don kuwa idan ka sayo magani daya, ta yiwu ba zai yi aiki ba. Shi ya sa muke da fargaba a wajen nan namu.
Source: BBC Hausa
Title :
Kullun Sai Nayi Jana'izar Wanda Maciji Ya Sara-Liman
Description : Daya daga cikin limaman addinin musulunci na Asibitin kula da mutanen da maciji ya sara a cikin jihar Gomben Najeriya, Malam Tukur Tela ya c...
Rating :
5