Shugaban Amurka Donald Trump ya fada wa sakataren harkokin wajensa cewa ya daina ɓata lokacinsa wajen tattaunawa da Koriya Ta Arewa game da shirinta na nukiliya.
"Ka daina wahalar da kanka Rex, za mu yi abin da ya kamata!" Shugaba Trump ya fada a wani saƙon Twitter, bayan ta bayyana cewa Amurka na tuntubar gwamnatin birnin Pyongyang.
Rex Tillerson ya bayyana wannan ci gaba ne ranar Asabar, ya ce Koriya Ta Arewa tana dan nuna sha'awar shiga tattaunawa.
Kasashen guda biyu sun yi musayar zafafan kalamai a watannin baya-bayan nan.
Amurka dai na son Koriya Ta Arewa ta dakatar da shirinta na kera makamai, wanda ya kai ta ga yin gwajin makamai masu linzami a karo da dama.
Bugu da kari, kasar ta ma yi ikirarin samun nasara gwada wani dan kankanin bam din Hydrogen wanda za a iya dora shi a kan makami mai linzami da ke cin dogon zango.
Sai dai kokarin hawa teburin sulhu ga alama ya ci karo da ra'ayin Shugaba Trump a kan wannan al'amari.
A ranar Lahadi ya aika sakon Twitter, dangane da jagoran Koriya Ta Arewa Kim Jong-un: "Na fada wa Rex Tillerson, sakataren wajenmu mai kokari, cewa yana bata lokacinsa kan yunkurin tattaunawa da Karami Mai wasa da garwashi..."
Mista Trump dai bai yi karin haske ba, kan abin da yake nufi da "za mu yi abin da ya dace".
Sai dai, wani babban jami'in Amurka, da aka nemi ya fayyace abin da hakan ke nufi, ya fada wa kamfanin dillancin labarai na Reuters: "A lokacin da Koriya Ta Arewa ke ci gaba da takalar fada, shugaban kasa ba ya tunanin lokaci ne yanzu da za a yi wata tattaunawa da su."
Jami'in ya ce an yi amfani da tuntubar diplomasiyyar akasari don tattauna batun Amurkawan da gwamnatin Koriya Ta Arewa ke tsare da su ne.
'Ku kasa kunne'
Ba karon farko kenan ba da kalaman Donald Trump ke son cin karo da manyan jami'ai a gwamnatinsa.
A cikin watan Agusta, ya ce sojojin Amurka sun "daura damara" don koya wa Koriya Ta Arewa hankali, sa'o'i bayan sakataren tsaronsa ya yi kokarin rage zaman dar-dar ta hanyar cewa kokarin diplomasiyya na samun nasara.
Kalamansa sun zo ne kwana guda bayan Mista Tillerson ya bayyana cewa jami'an Amurka sun bude wasu kafofin sadarwa da mahukuntan Pyongyang, duk da zafafar cacar-baki a tsakanin shugaban kasashen guda biyu.
Da aka tambaye shi ko Koriya Ta Arewa za ta hau teburin tattaunawar, sakataren wajen ya ce: "Muna turzawa, don haka ka kasa kunne."
Sai dai, daga bisani ya ce nasarar da aka yi 'yar kadan ce.
Rex Tillerson na wannan jawabi ne yayin wata ziyara da ya kai China, babbar abokiyar huldar kasuwanci da Koriyar Arewa, don ganawa da Shugaba Xi Jinping da sauran jami'ai.
A cikin makon jiya ne, China ta fada wa harkokin kasuwancin Koriya Ta Arewa da ke cikin iyakarta su rufe a wani bangare na sabbin takunkuman Majalisar Dinkin Duniya a kan wannan kasa mai taurin kai.
Source: BBC Hausa
Title :
Ku Barni Da Koriya Ta Arewa Kawai-Trumph
Description : Shugaban Amurka Donald Trump ya fada wa sakataren harkokin wajensa cewa ya daina ɓata lokacinsa wajen tattaunawa da Koriya Ta Arewa game da ...
Rating :
5