Kotu a jihar Legas da ta yanke hukuncin a tsare dan tsohon mataimakin shugaban Kasa Atiku Abubakar a dakin ajiye firsinoni ta sake shi, sai dai da sharadin zai dawo wa Fatimo, tsohuwar matar sa ‘ya’yan su.
An tsare Aminu ne a yau Laraba, bayan yanke hukuncin ayi haka da kotun Majistare da ke unguwar Tinubu, a Legas.
An tuhumi Aminu da bijire wa umarnin da mai shari’a Kikelomo Ayeye ta ba shi a ranar 11 Ga Oktoba, 2017, da ya gabatar da dan sa da ya dauke daga tsohuwar matar sa Fatimo Bolori.
A ranar 11 Ga Oktoba ce alkali Ayeye ya umarce shi da ya gabatar da yaron mai suna Amir mai shekaru shida, yau Laraba a kotu domin a fara sauraren karar da ke tsakanin sa da matar sa Fatimo da suka rabu tun 2011.
Source: Premium Hausa
Title :
Kotu Tasaki Dan Atiku
Description : Kotu a jihar Legas da ta yanke hukuncin a tsare dan tsohon mataimakin shugaban Kasa Atiku Abubakar a dakin ajiye firsinoni ta sake shi, sai ...
Rating :
5