A Najeriya, kotun tarayya dake Abuja ta umurci Sanata Enyinnaya Abaribe da wasu mutum biyu da suka yi belin Shugaban kungiyar 'yan ware ta Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu da su kawo shi gaban kotun.
Sauran mutum biyu da suka suka karbi belin jagoran kungiyar IPOB su ne Immanuel Madu da kuma Torchokwu Uchendu.
Mai shari'a Binta Nyako,ta bada umurnin ne ranar Talata lokacin da lauyan jagoran kungiyar Mr Ifeanyi Ejiofor ya shaidawa kotu cewa bai san inda wanda yake kare wa yake ba.
Shi dai Nnamdi Kanu da ake zargi da cin amanar kasa da mutanen uku suka tsaya masa beli bai halarci zaman kotun ba a ranar Talata don ci gaba da yi masa shari'ar.
Mai shari'a Binta Nyako ta ce matukar wadanda suka tsayawa Mr Kanu suka kasa kawo shi gaban kotun, zasu rasa Naira miliyan 100 da suka ajiye cikin sharuddan belin.
Tun da farko lauyan gwamnati Mohammed Labaran, ya bukaci kotun ta bada iznin sake kamo Nnamdi Kanu saboda ya saba ka'idojin belin da kotun ta shimfida masa.
Sai dai Lauyan Mista Kanu, Ifeanyi Ejiofor, ya ce bai san ko mutumin da ya ke karewa ya mutu ko kuma yana raye ba.
Ya ce tun da aka kai samame gidan da Mista Kanu yake zaune a watan Satumba ba su sake ganin shi ba.
Sai dai lauyan gwamnati ya nemi a dage shari'ar tun da dai lauyan Kanu ba zai iya gabatar da shi ba.
Wakilin BBC daya halarci zaman kotun, Ishaq Khalid, ya ce tun bayan da aka bude zaman kotu a ke ta tafka muhawara kan wannan batu.
Bayan sauraren duk bangarorin biyu, kotu ta dage zaman shari'ar zuwa ranar 20 ga watan Nuwamba.
A watan Afrilu ne aka bayar da belin Mista Kanu bayan ya shafe wata 18 a tsare.
Ba a dai sake ganin sa a bainar jama'a ba tun bayan rikicin da aka yi tsakanin jami'an tsaro da magoya bayansa a watan Satumba.
Wannan wata shari'a ce da ke cike da sarkakiya kuma tana iya kara tayar da zaune tsaye a kudu maso gabashin Najeriyar.
Wani abin da ya ja hankali shi ne bayanin da lauyan wanda ake kara ya yi cewa bai san inda mutumin da ya ke karewa ya ke ba.
Ifeanyi Ejiofor ya kara da cewa rabonsa da Mista Kanu tun lokacin da sojin Najeriya suka kai samame gidanshi a watan Satumba.
Rundunar sojin kasar ta dade tana musanta cewa shugaban na Ipob din na hannunta.
A yanzu da aka dage shari'ar, abin jira a gani shi ne ko Nnamdi Kanu zai bayyana a nan gaba, kuma wane mataki bangarorin za su dauka.
Source: BBC Hausa
Title :
Kotu Tabada Daman Akawo Mata Nnamdi Kanu
Description : A Najeriya, kotun tarayya dake Abuja ta umurci Sanata Enyinnaya Abaribe da wasu mutum biyu da suka yi belin Shugaban kungiyar 'yan ware ...
Rating :
5