Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai je kasar Turkiyya ranar Laraba don halartar taron koli na kasashe masu tasowa wato D8 da za a fara ranar Juma'a.
Wata sanarwa da mai bai wa Shugaba Buhari shawara kan harkokin watsa labarai Femi Adesina ya fitar, ta ce gabannin taron shugaba Buhari ya samu gayyata daga shugaban Turkiyyar Recep Tayyip Erdogan don ziyarar aiki a birnin Ankara.
Sanarwar ta ce bayan gana wa da shugaban Najeriyar zai yi da shugaba Erdogan, 'yan tawagar shugaban kasar za su tattauna da takwarorinsu na Turkiyya kan batutuwan da suka hada da tsaro, da ilimi da kuma batun 'yan ci-rani.
Yayin ziyarar, Shugaba Buhari zai je Majalisar Dokokin Turkiyya a birnin Ankara inda zai gana da kakakin Majalisar Ismail Kahraman.
Sanarwar ta kara da cewa, lokacin taron koli na kasashe masu tasowar da za'a gudanar a birnin Santanbul da cibiyar kasuwancin Turkiyyar, Shugaba Buhari zai yi amfani da damar wajen kara karfafa dangantaka tsakanin Najeriyar da sauran shugabannin kasashen da ke kungiyar.
Kasashen su ne, Bangladesh da Masar da Indonesia da Iran da kuma kasar Malaysia.
Sauran kasashen su ne, Pakistan da kuma Turkiyya mai masaukin baki.
Daga cikin 'yan tawagar Shugaba Buhari sun hada da wasu ministoci da manyan jami'an gwamnati da kuma shugaban hukumar kwastam ta Najeriya, kanar Hameed Ali mai ritaya.
Ana sa ran jami'an gwamnatin Najeriya za su tabo batun kame makamai da hukumar kwastam ta yi wadanda aka shigo da su kasar daga Turkiyyar yayin tattaunawar da za su yi.
A baya-bayan nan dai hukumar kwastam ta Najeriya ta kama bindigogi 470 a tashar jiragen ruwan Tincan Island a Lagos, wadanda aka shigo da su daga kasar Turkiyya, makonni kadan da aka kama wasu fiye da 1,000 da suma aka shigo da su daga Turkiyyar.
Gwamnatin Najeriyar dai ta ce dole ta hau teburin tattauna wa da ofishin jakadancin Turkiyya da ke kasar.
Wannan ne dai karo na biyu da Shugaba Buhari zai je wata kasa tun bayan dawowarsa jinyar wata uku daga Birtaniya.
Source: BBC Hausa
Title :
Kome Buhari Yajeyi A Turkiyya?
Description : Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai je kasar Turkiyya ranar Laraba don halartar taron koli na kasashe masu tasowa wato D8 da za a fara ra...
Rating :
5