Dangin wasu matasa da ke cikin mutanen da gwamnatin Najeriya ke tuhuma 'yan Boko Haram ne sun ce sun ji dadi da fara jerin shari'o'in irin wadannan mutane a kasar cikin wannan mako.
An dai yi zaman shari'ar farko ne ranar Litinin a wani kurkuku da ke garin Kainji na jihar Neja da ke arewacin kasar.
Mutane kimanin 800 da ake tuhumarsu da zama 'yan Boko Haram ne, aka gurfanar gaban kotu a Litinin din nan, rana ta farko ta fara shari'ar gama-gari ga dubban irin wadannan mutane da hukumomin Najeriya suka yi.
Malam Yusuf Salihu Oga mazaunin garin Doma cikin jihar Nassarawa wanda wasu danginsa ke tsare a kurkukun Ka'inji tun shekara ta 2014, ya zargi hukumomi da kin bin umarnin kotu.
Ya ce a kai su kotu idan (hukumomi suna da tuhuma), su kuma wadanda aka sallame su idan DSS ba su yarda ba, sai su daukaka kara.
Yusuf Oga ya ce rashin sanin ko 'ya'yansu na daga cikin mutanen da za a gurfanar gaban kotu a yanzu, babban abin damuwa ne gare su.
A cewarsa: "Idan mun kai watan Fabrairu mai zuwa, yaranmu na da shekara hudu a tsare kenan."
"Cikin watan biyu na shekarar 2014 ne hukumomin tsaro suka zo suka kama wani danmu mai suna Umar Ibrahim, washe gari kuma suka dawo suka kama wasu," in ji shi.
Ya ce al'amarin ya jefa fargaba a zukatan matasan garin, lamarin da ya sa wasu da dama suka yi kaura suka gudu.
Malam Yusuf Oga ya ce tsawon lokaci ba su san inda ake tsare da yaransu, sai lokacin da wani abokin zaman wakafinsu da kotu ta sa aka sake shi, ya je ya fada musu.
"Yaranmu ne suka ba wannan abokin nasu da suka zauna sarka a kurkukun soja ta Ka'inji sakon cewa ya je ya fada wa iyayensu cewa suna nan a raye, kuma ga inda suke."
Ya ce daga nan mu ma sai muka je kotu muka yi kara.
"Kotu ta ba da belin mutum hudu na farko, kuma a watan uku kotu ta sallami sauran mutum hudu da ke tsare a Ka'inji, ko da yake har yanzu ba a sake su ba."
Source: BBC Hausa
Title :
Koda 'Ya'yan Mu A Cikin Wadanda Ake Wa Shari'ar Boko Haram?
Description : Dangin wasu matasa da ke cikin mutanen da gwamnatin Najeriya ke tuhuma 'yan Boko Haram ne sun ce sun ji dadi da fara jerin shari'o...
Rating :
5