An yi ta watsa sanarwar gwamnati a shafukan sada zumunta jim kadan bayan da shugaba Robert Mugabe ya sanar da kafa wata ma'aikata da za ta maida hankali wajen samar da tsaro a harkar Internet.
Al'ummar Zimbabwe dai sun yi ta raha kan wasikar wacce ke dauke da sa hannu da kuma adireshi na boge na sabon ofishin ministan samar da tsaro a harkar Internet, Mr Patrick Chinamasa wanda ke umurtar duk masu amfani da WhatsApp a matsayin dandali da su yi rijista a ma'aikatar nan da watan Nuwamba.
Sai dai yanzu an rage yawan raha da ake yi kuma 'yan kasar Zimbabwe sun maida hankali wajen nazarin tasirin sabuwar ma'aikatar musamman kan batun da ya shafi 'yancin fadin albarkacin baki.
'Barazana ga Kasa'
Gwamnatin Zimbabwe dai na dari-dari da yadda ake amfani da shafukan sada zumunta tun bayan da a shekarar data gabata, wani Fasto Evan Mawararire ya jagoranci wani gangami da aka rika amfani da maudu'in #ThisFlag movement.
Ta hanyar shafukan sada zumunta na Twitter da Facebook an shirya gangami na zama a gida, gangamin da shi ne mafi girma na kin jinin gwamnati da aka taba shirya wa a 'yan shekarun nan.
Kakakin shugaban kasar Mr George Charamba, ya ce shugaba Mugabe ya yanke shawarar kafa ma'aikatar ce don shawo kan sabuwar barazanar da kasa ke fuskanta wanda ya ce ''ana tsara wa da kuma daukar nauyi don aikata ayyukan da ba su kamata ba".
Da alamu dai shafukan sada zumunta su ne hanyoyin farko da al'ummar Zimbabwe ke amfani wajen mu'amala tare da samun labarai.
Wannan hanya dai ta na cigaba da bunkasa duk kuwa da dokokin takaita fadin albarkacin baki.
A cikin shekaru 16 da suka gabata, amfani da Internet a kasar ya karu daga kashi 0.3% zuwa kashi 46%, kamar yadda kididdiga daga hukumar sadarwa ta nuna.
Gidajen talbijin da kuma jaridu na Internet har da wadanda suke aiki daga wasu kasashen waje na amfani da Internet don watsa labarai da gwamnati ba ta da iko akai.
A lokacin da gidajen sayar da man fetur suka rasa mai a watan daya gabata, an yi ta ganin dogayen layukan a manyan shagunan Zimbabwe inda 'yan kasar ke rige-rigen sayen abinci don kaucewa karancin sa.
Gwamnati dai ta yi zargin cewa an yi amfani da shafukan sada zumunta wajen yada sakonnin karya da suka firgita jama'a.
'Kokarin hana fadin ra'ayi'
Sai dai wasu na ganin cewa matsayin gwamnati kan wannan batu tamkar barazana ce ga 'yancin fadin albarkacin baki da kuma walwala.
Wata kungiya kan yancin sadarwa a Zimbabwe ta reshen cibiyar yan jaridu a ynkin kudancin Afrika a wata sanarwa, ta ce wannan sabon bincike kan kafafen sada zumunta ya sabawa kundin tsarin mulki da kuma yancin fadin albarkacin baki.
Sanarwar ta kara da cewa, ''abun takaici barazanar da ake yi ta janyo mutane na takaita yadda suka tattauna al'amurran da suka shafi kasa."
Kungiyar ta kuma suko takunkumi da ake sanya wa kafafen yada labarai a Zimbabwe saboda kawai suna ba jama'a damar fadin ra'ayin su a shafukan Internet kan rahotanni da kafafen suka gabatar.
A nata bangaren, gamayyar jam'iyyun adawa a Zimbabwe, Movement for Democratic Change (MDC) ta ce sabuwar ma'aikatar tsaro a harkar Internet da gwmanati ta kafa, wata hanya ce ta rika yi wa jama'a leken asiri.
Jagoran gamayyar jam'iyyun adawar Morgan Tsvangirai ya yi amannar cewa an kafa ma'aikatar ce don takaita 'yancin fadin albarkacin baki yayin zabubbukan 2018.
Ya ce "Shugaba Mugabe... zai yi duk abun da zai iya yi don dakile shafukan sada zumunta saboda ya hana tasirin korafin da jama'a ke yi kan gwamnatin sa,".
"Koda yake a cewar sa, babu yadda gwamnati zata yi don dakile shafukan sada zumunta."
Za'a tsare mutane nan gaba?
Yayin da wa su kasashen duniya da dama su ke da hukumomi wadanda ke yaki da masu aikata laifuffuka ta shafin Internet, Zimbabwe ce kasa ta farko a duniya da ta kafa ma'aikata sukutum da guda don kula da hakan.
A yanzu dai ana cigaba da yada sakonni na gargadi a shafukan sada zumunta.
Misalin irin wadannan sakonni shi ne daga wani mutum mai suna "Mr Chaipa", wanda ya bukaci 'yan Zimbabwe da suka rika yada labaran da za su iya kare kansu a gaban kotun ne kadai a shakukan sada zumunta.
Mr Chaipa ya ce yana da sauki gwamnati ta sa ido kan sakonni da ake watsawa inda ya lissafa jerin ayyuka ta Internet da za'a iya dangantawa a matsayin manyan laifuffuka.
''Nan da wa su watanni ma su zuwa za'a kame mutane da dama don su zama abun misali da za su sa mutane suk guji wuce makadi da rawa a lokacin da su ke amfani da shafukan sada zumunta gabannin zabe," in ji shi. "
Source: BBC Hausa