An ayyana Shugaban Kenya, Uhuru Kenyatta, a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar mai cike da ce-ce-ku-ce.
Ya lashe kashi 98 cikin 100 na kuri'un da aka kada yayin da masu kada kuri'u kasa da kashi 39 cikin 100 suka fito- kasa da rabin wadanda suka kada kuri'a a zaben watan Agusta, in ji hukumar zaben kasar.
Jagoran 'yan adawa, Raila Odinga, ya janye daga zaben da aka sake yi kuma ya bukaci mabiyansa su kaurace wa zaben.
Ko a zaben da aka yi watan Agusta ma, an ayyana Mista Kenyatta a matsayin wanda ya lashe zaben wanda aka soke bisa dalilai na magudi.
Kuma an dakatar da zaben a mazabu 25 domin fargabar rashin tsaro.
Hukumar ta ce sakamakon wadannan mazabun ba zai shafi sakamakon zaben ba, don haka ne ta bayyana sakamakon zaben.
Shugaban hukumar zaben, Wafula Chebukati, ya bayyana zaben na baya-bayan nan a matsayin sahihin zabe.
Bangaren adawa na Kenya dai yana da kwanaki bakwai don kalubalantar zaben, kuma Mista Odinga ya ce zai yi wata sanarwa a ranar Talata.
Source: BBC Hausa
Title :
Kenyatta Ya Sake Lashe Zaben Kenya
Description : An ayyana Shugaban Kenya, Uhuru Kenyatta, a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar mai cike da ce-ce-ku-ce. Ya lashe kashi 98 cikin 1...
Rating :
5