Mai ba gwamnan jihar Katsina, Aminu Masari kan Kasafin Kudi Abdullahi Imam ya ce gwamantin jihar ta bada gudunmawar Naira miliyan 350 wa hukumar UNICEF domin kula da yaran dake fama da yunwa a jihar.
Yayin da yake sa hannu a yarjejeniyar da gwamnatin jihar ta yi da hukumar UNICEF Abdullahi Imam yace gwamnatin ta yi haka ne don bada nata gudunmawar wajen ganin an kawo karshen wannan matsala da ake fama dashi.
Ya ce gwamnatin jihar za ta ci gaba da bada gudunmawarta don kula da yaran dake fama da yunwa a jihar daga cikin kasafin kudinta na shekarar 2018.
Yayin da take mika godiyar ta ga gwamnatin jihar jami’ar hukumar UNICEF Padmavathi Yedla ta ce wannan gudunmawar da gwamnatin jihar Katsina ta bayar da wanda gidauniyar ‘Children Investment Fund Foundation (CIFF)’ abu ne da ya cancanci a jinjina musu gaba daya.
Ita ma asusun CIFF ta bada gudunmuwar naira miliyan 350 domin wannan shiri na kauda yunwa da talauci a jihar.
Kamfanin Dillancin labaran Najeriya ta ce hukumar UNICEF ta fara raba katan-katan har kusan 30,000 na abinci wa yaran dake fama da yunwa a kananan hukumomi 15 a jihar.
Source: Premium Hausa
Title :
Katsina Tabada Miliyan 350 Don Kula Da Yaran Dake Fama Da Yunwa A Jihar
Description : Mai ba gwamnan jihar Katsina, Aminu Masari kan Kasafin Kudi Abdullahi Imam ya ce gwamantin jihar ta bada gudunmawar Naira miliyan 350 wa huk...
Rating :
5