Galibin muhawara da ake yi game da makarantu a kasashen da suka ci gaba ana yi su ne a kan siyasar me ya kamata a fi bai wa muhimmanci, wadanne darussa za a fi bai wa muhimmanci, wa yake da bukatar karin taimako, kuma wanne bangare ne ya fi bukatar gwamnati ta fi kashe wa kudi.
Sai dai ga iyalai da dama a yawancin kasahen da suka ci gaba, batun ilimi bai ma kai haka ba, to babbar tambayar ma ita ce ko ana samun damar zuwa makarantar?
Alkaluma daga Majalisar Dinkin Duniya (MDD) sun nuna cewa, ba a samu wani ci gaba ba a shekara 10 da suka shude wajen yaki da rashin guraben karatu a wasu kasashen da suka fi talauci a duniya.
Wani rahoton kuma ya bayyana darajar ilimi, kuma MDD ta ce abin da aka gano din, da kusan sama da yara miliyan 600 ne suke makaranta amma ba sa koyar komai.
Ko da yake a wasu kasashen yamma, mata sun sha gaban maza a karatu, amma a yankin kasashen da ba su da arziki a duniya, musamman yankin Saharar Afirka, alamu sun nuna ba lallai ne mata su samu damar karatu ba.
Yankunan da ake rikici
A fadin wadannan kasashe 10, yawanci daga cikin wadanda ba su da gurbin karatu yara mata ne.
Wadannan kasashe ne masu rauni, inda iyalai da dama ke fuskantar talauci da rashin lafiya da rashin abinci mai gina jiki da kuma rashin matsugunni sakamakon yaki da tashin hankali.
Yara mata da dama sun fi yin aikatau maimakon su tafi makaranta. Kuma yawanci an fi aurar da kananan yara, inda daga karshe ba z asu samu damar yin karatu ba.
Alkaluman MDD sun nuna cewa yara mata da dama ne ke fuskantar barazanar rashin samun ilimi a yankunan da suke fuskantar rikici.
A wasu kasashe irin su Siriya, babu isassun bayanai daga majiya mai tushe daga wurinsu da za a saka su a cikin lissafi.
Wadannan ne kasashe 10 da yara mata suke fuskantar barazanar ilimi:
1. Sudan Ta Kudu: Ita ce kasar da ta fi ko wacce fuskantar rikici a duniya, da rushe makarantu da kuma raba iyalai da muhallinsu, kusan kashi daya bisa uku na yara mata a kasar ko makarantar firamare ba sa zuwa.
2.Jamhuriyar Tsakiyar Afirka: Dalibai 80 ne a karkashin malami daya
3.Nijar: Kashi 17 cikin 100 na mata tsakanin shekara 15 zuwa 24 ne kawai suka yi karatu.
4.Afghanistan: Akwai tazara mai nisa tsakanin maza da mata domin maza sun fi mata zuwa makaranta.
5.Chad: Abubuwa da dama da suka hada da talauci na hana mata da 'yan mata samun ilimi
6.Mali: Kashi 38 cikin 100 na mata ne kawai suke kammala karatun firamare
7.Guinea: Lokacin da mata da suka haura shekara 25 ke amfani da shi wajen koyon ilimi bai wuce shekara daya ba
8.Burkina Faso: Kashi daya cikin 100 na mata ne kawai suke kammala makarantar sakandare
9.Liberia: Kusan kashi daya bisa uku na shekarun 'yan firamare ba sa zuwa makaranta
10. Habasha: Mata biyu daga cikin biyar suna yin aure kafin shekara 18
Karancin malamai ya zama ruwan dare a kasashen da suke fama da talauci.
A bara ma, MDD ta ce ana bukatar wasu malamai miliyan 69 a fadin duniya zuwa shekarar 2030, idan har alkawuran da kasashe suka yi a kan ilimi ya tabbata.
Rahoton ya ce akwai bukatar karkasa tattalin arziki muddin ana so yara mata su je makaranta.
Kuma ko wanne zai samu kaso mai gwabi, kamar su Florence Cheptoo, wacce ta zauna a wani kauye mai nisa a Kenya kuma ta koyi karatu tana da shekara 60.
Gayle Smith shugaban wata kunigyar fafutuka, ya ce: "Sama da yara mata miliyan 130 ne yanzu haka ba sa zuwa makaranta, kuma a cikinsu za a iya samun injiniyoyi da malamai da manyan 'yan kasuwa da 'yan siyasa da zasu shugabanci duniya."
Source: BBC Hausa
Title :
Kasashen Da Mata Ke Wahalan Samun Ilimi A Duniya
Description : Galibin muhawara da ake yi game da makarantu a kasashen da suka ci gaba ana yi su ne a kan siyasar me ya kamata a fi bai wa muhimmanci, wada...
Rating :
5