Ikirarin: Kare a Amurka ya fi samun damar a yi masa gashin cutar sankara fiye da mutum a Najeriya.
Gaskiyar lamarin: Na'u'rorin kashe kwayoyin cutar sankara da ake da su domin mutane a Najeriya ba su kai wadanda aka tanada domin karnuka a Amurka ba.
Amman sai dai dabbobi 'yan lele masu dauke da cutar sankara a Amurka sun fi mutane masu cutar samun gata a Najeriya - kuma na'u'rorin kona cutar sankara da ake da su na dabbobi kawai sun fi na wadanda ake amfani da su gutanen Najeriya.
A watan da ya gabata ne, Sean Murphy ya janyo ce-ce-ku-ce a shafukan sa da zumunta.
Dan kasuwar ya wallafa wani hoton kare da yake amfani da wata irin na'u'rar konaa cutar sankara, kuma ya ce irin wadannan na'u'rorin da ke yi wa karnukan Amurka magani sun fi wadanda suke yi wa 'yan Najeriya magani.
Ya ce wannan na nufin kare a Miami ya fi wata mata a Legas damar samun maganin sankara. Maganar tasa ba ta zo wa mutane da dama da mamaki ba, amman duk da haka ta fusatansu
Amman da alamar gaskiya a ikirarin nasa? Shin karnukan Amurka sun fi 'yan Najeriya damar samun na'u'rar kona sankara?
Kayan aiki
Ba ko wanne mai cutar sankara ke bukatar gasa sankara ba - akwai wasu nau'o'i na magani, irin su hanyar shan magani domin dakile cutar sankara.
Amman ikirarin Mista Murphy ya yi ne kan damar samun na'u'rar kona sankara, saboda haka bari mu tsaya a kan wannan na'urar kawai.
Hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya tana da jerin sunayen wuraren da ke da na'u'rorin gasa sankara a fadin duniya.
Matattarar bayanan cibiyoyin na'urorin gasa sankara ta hukumar (Dirac) tana samun bayanai ne daga kasashe daban-daban. Amman a makon da ya gabata ne kawai aka tattara bayanai na baya-bayan nan.
Matattarar ta ce abun ya fi yadda Mista Murphy ya bayyana shi muni.
Nau'rorin gashi uku ne ke aiki a Najeriya a halin yanzu, kuma babu na zamani irin wanda Mista Murphy ya ambato a sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter.
Dirac ta ce a kan hada na'ura ta hudu a Abuja, kuma wannan din ma ba za ta kasance irin ta zamani da Murphy ya ambata ba.
Akwai karin na'u'rori da ake amfani da su wajen shirya ba da magani irin su na'u'rorin daukar hoton kashi.
Kuma Dirac ta ce babu wata cibiyar ba da magani da ta sani da take bai wa mara lafiya gashi kan dashe, wadda ita ce hanyar ba da maganin cuta irin sankarar mahaifa.
Babu tabbacin karin na'u'rorin nawa ne za a iya samu a asibitoci masu zaman kansu - amman jaridar The Nation ta ce wadannan sun fi karfin mara sa galihu.
Bayanai daga bankin duniya sun nuna cewar yawan mutane a Najeriya ya kai miliyan 186. Da zarar an kammala hada na'u'rar ta hudu, za a samu na'urar gashi daya ga mutum miliyan 46.5 a Najeriya.
Idan ma na'urori takwas da Najeriya ta ke da ita a shekarar 2010 suna aiki har yanzu - adadin mutanen da za su dogara da na'u'rar gashi daya zai kai mutum miliyan 23.2 .
A Kenya, akwai na'urar gashi daya ga mutum miliyan 5.4 million.
A Indiya kuma mutum miliyan 2.2 suna da na'ura daya, ga mutum 188,000 suna da na'urara gashi daya a Birtaniya yayin da mutum 84,000 ke da na'urara gashi daya a Amurka.
Source: BBC Hausa
Title :
Karnukan Amurka Sunfi 'Yan Nigeria Gata A Asibiti
Description : Ikirarin : Kare a Amurka ya fi samun damar a yi masa gashin cutar sankara fiye da mutum a Najeriya. Gaskiyar lamarin : Na'u'rorin...
Rating :
5