A kalla mutum 12 ne suka mutu bayan da wani jirgin ruwa dauke da Musulman Rohingya ya kife a teku kusa da Bangladesh, a cewar jami'ai.
Mutane da yawa sun bata bayan hatsarin da ya afku a kogin Naf a ranar Lahadi. Ana tsammanin cewa, mutum 100 ne ke cikin jirgin, da suka hada da yara.
Dama dai gomman mutane ne suka mutu a kokarinsu na tsallakawa zuwa Bangladesh saboda 'gallazawar' da sojoji suke musu a jihar Rakhine ta Myanmar.
Har yanzu ba a san adadin yawan mutanen da ke cikin jirgin ba wanda ya kife ranar Lahadi, sai dai jami'an da ke kula da kan iyakar Bangladesh suna ba da kiyasin cewa a kalla za su kai mutum 40 zuwa 100.
Wannan shi ne iftila'i na baya-bayan nan da ya faru na hatsarin jiragen ruwa da ke dauke da 'yan ci-ranin Rohingya zuwa Bangladesh.
Ana zaton a kalla mutum 60 sun mutu a irin wannan iftila'i a karshen watan Satumba.
Mutane da yawa sun yi amfani da iyakar Banladesh ta kasa, inda wadansu kuma suke kokarin tsallaka iyakar Banladesh ta hanyar teku a cikin kananan jiragen ruwa na masu kamun kifi.
Mai magana da yawun wata cibiyar bayar da agaji ta 'Save The Children' Evan Schuuram, ya ce; "Har yanzu mutane da yawa suna son su shiga jiragen da suka cika, mutanen da ba su iya ninkaya ba, suna sa kansu cikin hatsari don su tsallaka zuwa Bangladesh."
Daga Bangladesh, Mista Schuuran ya fada wa BBC cewa rikicin 'yan ci-rani ya zama 'wani babban bala'i da ke shafar yara.'
"Daya daga cikin hujjojin da suka bayyana sosai, shi ne idan kana tafiya a cikin sansanonin 'yan Rohingya za ka ga yara da ke cikin damuwa da tashin hankali."
Kalli bidiyon da aka dauka daga jirgi mara matuki da ke nuna sansanonin 'yan ci-ranin Rohingya a Bangladesh
An yi tashin hankali a jihar Rakhine a karshe-karshen watan Agusta, yayin da mayakan sa kai na Rohingya suka kai hari wajen jami'an tsaro, abin da ya jawo sojoji mayar da martani.
'Yan Rohingya fiye da rabin milliyan ne suka tsere zuwa Bangladesh saboda an hana su 'yancin zama 'yan kasa a Myanmar.
Ana zargin sojojin Myanmar da aikata kisan kare dangi kan Musulman Rohingya, amma sun ki amincewa da wadannan zarge-zarge.
Source; BBC Hausa
Title :
Jirgin Ruwa Yakife Da Yara Musulman Rohingya
Description : A kalla mutum 12 ne suka mutu bayan da wani jirgin ruwa dauke da Musulman Rohingya ya kife a teku kusa da Bangladesh, a cewar jami'ai. ...
Rating :
5