Wani masani ya ce tattalin arzikin Najeriya bai yi farfadowar da za a ce kasar ba ta bukatar ciyo bashi daga kasashen waje don samar da ayyukan raya kasa ba.
Da yake zantawa da BBC, Malam Yusha'u Aliyu ya ce ko da yake tattalin arzikin Najeriya ya fita daga matsi mafi muni da ya fuskanta a tsawon shekaru, amma sai ya cim ma bunkasar kashi 35 cikin 100 kafin ta iya warware matsalolinta da kanta.
"Ba a fita ba gaba daya, sai ya samu managarciyar bunkasa kafin Najeriya ta kai matakin da za ta iya yin komai da dan abin da take samu."
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ne ya nemi amincewar Majalisar dattijan kasar don karbo bashin dala biliyan 5.5.
A wata wasika da ya aike wa Majalisar, Shugaba Buhari ya ce daga ciki kudaden, za a yi amfani da dala biliyan 2.5 ne don sayen takardun lamuni daga kasashen Turai a kasuwannin duniya.
Malam Yusha'u Aliyu ya ce dole akwai bukatar kudade makudai don a tallafa wa tattalin arzikin Najeriya ta yadda zai iya murginawa yadda ake so.
Masanin tattalin arzikin ya ce duk kasafin kudi a duniya yana zuwa da gibi na bashi.
"Muhimmin abu shi ne tun da kasuwar canji ta fara daidaita a kasar yanzu karbo bashin kasashen waje zai fi tasiri maimakon a baya," in ji shi.
A cewarsa wajibi ne a ciyo bashi amma amma sai an yi la'akari a wajen wa za a ciyo bashin? Da kuma wadanne irin yanayi ne a tattare da bashin.
Haka zalika, abin dubawa ne a san me za a yi da bashin idan an ciyo.
Ya ce kamata ya yi a auna a gane abin da ya janyo matsin tattalin da kasar ta yi fama da shi da kuma abubuwan da suka janyo ta fita daga cikinsa.
Yusha'u Aliyu ya ce sai gwamnati ta zuba kudade a fannonin da za su taimaka wajen bunkasa tattalin arziki da kuma kula da ma'aikata.
Tun da farko, shi a zantawarsa da BBC, Shugaban Kwamitin kula da basuka na kasashen waje a majalisar dattijan Najeriya Sanata Shehu Sani ya ce sai bangaren zartaswa ya yi musu bayanin abin da zai yi da karin bashin dala biliyan uku kafin majalisar ta amince.
Ya ce abin da aka ce za a biya cikin shekara 30 zuwa 50, ba shakka 'ya'yanmu da jikokinmu za su zo su yi tambaya su ce me aka yi da wannan abu.
A cewarsa za su gayyaci ministar kudi, Kemi Adeosun da sauran bangarori, don yi musu bayani kan abin da za su yi da wannan kudi.
"Ta gaya mana yadda za a yi a biya wannan kudi ko bayan ba gwamnatinsu da kuma inda za a karbo bashin har ma da sharuddan da ke kansa."
Shehu Sani ya ce duk wadannan bayanai za su kasance a cikin rahoton da za su gabatar wa majalisa.
Source: BBC Hausa
Title :
Jikokin Mu Zasu Nemi Jin Me Akayi Da Wannan Bashin
Description : Wani masani ya ce tattalin arzikin Najeriya bai yi farfadowar da za a ce kasar ba ta bukatar ciyo bashi daga kasashen waje don samar da ayyu...
Rating :
5