Jami’an tsaron fadar shugaban Kasa sun hana shugaban majalisar Dattawa Bukola Saraki, Kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara da sauran shugabannin majalisun shiga fadar gwamnatin bayan tilasta su da jami’an tsaro suka yi cewa dole sai sun sauko daga motar da suka zo da shi kafin nan su wuce.
Bayan ‘yar takaddama da suka yi tsakanin su ‘yan majisan suka juya da motar su suka koma.
Bayan haka shuagaban ma’aikatan fadar gwamnati Abba Kyari da kansa ya tafi ya dawo da shugaban majalisar dattawa da na wakilai domin ganawa ta musamman da shugaban kasa Muhammadu Buhari.
‘Yan majalisar sun taho fadar gwamnatin ne don amsa gaiyatar shugaban kasa na su zo su ci abincin dare tare da shi.
Garba Shehu ya sanar mana cewa lallai an sami rashin jituwa da jami’an tsaron fadar amma an shawo Kan abin.
Source: Premium Hausa
Title :
Jami'an Tsaro Sun Hana Saraki Da Dogara Shiga Fadan Shugaban Kasa
Description : Jami’an tsaron fadar shugaban Kasa sun hana shugaban majalisar Dattawa Bukola Saraki, Kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara da sauran shug...
Rating :
5