Jami'ar Umaru Musa 'Yar'adu ta jihar Katsina ta bayar da aikin kame macizai daga makarantar da ke arewa maso yammacin Najeriya.
Babban jami'inmakaramtar mai lura da dalibai, Dr Suleiman Kankara, shi ne ya tabbatar da hakan.
Dr Kankara ya ce duk da cewa masu kama macijin ba su dade da fara aiki ba, jami'ar ta dade tana shirin ta dauke su a aiki.
Ya ce dama dai a duk lokacin da aka samu maciji a makarantar a kan kira masu kama maciji ne don su taimaka, amma yanzu za a dauke su aiki ne na ko yaushe.
A makon jiya ne dai maciji ya kashe wata budurwa tana dab da kammala karatunta a jami'ar.
Zainab Umar, daliba ce wacce take shekarar karshe a fannin nazarin tattalin arziki ta jami'ar Umar Musa 'Yar'adua ta jihar katsina kafin ta rasu.
Wata sanarwa daga hukumar jami'ar ta ce, maciji ya sari Zainab ne ranar Juma'a kuma an yi mata magani a asibitin da ke makarantar.
Sanarwar da jami'ar hulda da jama'a ta makarantar Fatima Sanda, ta sanya wa hannu ta ce a ranar Asabar ne iyayen marigayiyar suka dauketa daga jami'ar zuwa gida don yi mata maganin gargajiya.
Amma sai ALlah ya yi mata rasuwa a ranar Litinin.
Source: BBC Hausa
Title :
Jami'ar Katsina Zata Dauki Masu Kama Macizai Aiki
Description : Jami'ar Umaru Musa 'Yar'adu ta jihar Katsina ta bayar da aikin kame macizai daga makarantar da ke arewa maso yammacin Najeriya. ...
Rating :
5