Kungiyar IS mai ikirarin jihadi ta dauki alhakin kai hari wani kauye a jihar Yobe dake arewa maso gabashin Najeriya inda ta ce ta kashe akalla sojoji 15.
Ko da yake ba za a iya tantace iya mutum nawa suka mutu a harin ba.
A wata sanarwar da ta fitar ta Intanet da harshen larabci, kungiyar IS ta ce mayakanta sun far wa wani sansanin sojin Najeriya a jihar Yobe kuma sun yi awon gaba da makamai da kuma motocin soji hudu.
Rundunar sojin Najeriya dai ta tabbatar da cewa an kai harin kuma an samu mace-mace a bangarorin biyu, amman ba ta bayar da adadin wadanda suka mutu ba.
A baya dai, bangaren kungiyar Boko Haram da ke da alaka da kungiyar IS ya yi ikirarin cewa yana hakon jami'an tsaron Najeriya.
Boko Haram ta shafe kusan shekara goma tana kaddamar da hare-hare a arewacin Najeriya.
Gwamnatin Najeriya dai na ikirarin cewa ta kakkabe Boko Haram daga dajin Sambisa inda suka fi karfi a da.
Amman mayakan kungiyar suna ci gaba da kai hare-haren kunar bakin wake tare kai hare-hare kan jami'a tsaro da fararen hula, musamman ma a arewa maso gabashin Najeriyar.
Source: BBC Hausa
Title :
IS Tadauki Alhakin Harin Da Aka Kai Yobe
Description : Kungiyar IS mai ikirarin jihadi ta dauki alhakin kai hari wani kauye a jihar Yobe dake arewa maso gabashin Najeriya inda ta ce ta kashe akal...
Rating :
5