Hukumar zaben Najeriya ta dakatar da yunkurin yi wa Sanata Dino Melaye, mai wakiltar jihar Kogi ta yamma, kiranye daga majalisar dattawan kasar.
Hukumar ta dakatar da yunkurinne bayan sanatan ya ki ya karbi takardar sanarwar fara tantance wadanda suka kada kuri'ar cewa suna son a mishi kiranye daga mazabarashi.
A wata sanarwa da kwamishina mai kula da watsa labarai da fadakarwa a hukumar, Solomon Soyebi, ya sanya wa hannu, hukumar ta ce ya kamata a fara yi wa sanatan kiranye ne a ranar 3 ga watan Oktoba bisa sabuwar jadawalin da ta yi bayan kotu ta yi wasti bukatar sanatan na dakatar da kiranyen.
Saidai kuma kotun ta bai wa hukumar umarnin mika wa sanatan sanarwar kiranyen hannu da hannu, tare da bashi takardun da ke da alaka da yunkurin mishi kiranyen akalla mako biyu kafin a fara kiranyen.
Sanarwar hukumar ta ce jami'an hukumar tare da wani jami'in babban kotun tarayyar Najeriya sun je gida da ofishin sanatan sau shida, amman sun sami ofishinshi a kulle kuma ba su samu shiga gidansa ba.
Har wa yau sanarwar ta ce sanatan ya ki karbar takardun a gaban 'yan jarida bayan 'yan majalisa sun koma bakin aiki.
Hukumar ta ce ta garzaya kotu domin a bata izinin sanar da sanatan game da kiranyen ta wata kafa ta daban.
Amman kotun ta ce hukumar ta sake komawa ta yi kokarin bai wa sanatan sanarwar fara kiranyen hannu da hannu.
Da ta kasa mika mishi sanarwar, sai hukumar ta sake koma kotun wadda ta ce ba ta hurumin kan lamarin domin sanatan ya riga ya daukaka kara.
Domin ta kasa sanar da sanatan game kiranyen, hannu da hannu, hukumar ta ce ya zama dole ta dakatar da kiranyen har sai kotun daukaka kara ta yanke hukunci kan kararar da sanatan ya shigar.
A baya dai hukumar ta gudanar da zaben kiranye a mazabar sanatan domin gane ko yawancin mutanen mazabarsa suna son sanatan ci gaba da wakilcinsu ko kuma ya daina wakilcinsu a majalisar dattawan kasar.
Bayan wannan ne ya kamata hukumar ta tantance kuri'un wadanda suka kada kuri'a a zaben.
Source: BBC Hausa
Title :
INEC Tasake Dakatar Da Yiwa Dino Melaye Kiranye
Description : Hukumar zaben Najeriya ta dakatar da yunkurin yi wa Sanata Dino Melaye, mai wakiltar jihar Kogi ta yamma, kiranye daga majalisar dattawan ka...
Rating :
5