Shahararren attajirin nan kuma sirikin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Muhamadu Indimi ya na gina gidaje masu dakuna uku-uku a garin Bama don taimakawa ‘yan asalin garin Bama da suke sansanonin ‘yan gudun hijira.
Da yawa daga cikin mazauna sansanonin ‘yan gudun hijira na so su koma garuruwansu tun bayan zaman lafiya da aka samu a yankunan jihar da Boko Haram suka mamaye.
Mazauna garin Bama dai sun dade suna kokawa da a barsu su koma garunsu domin zaman sansanonin ya ishe su haka.
Indimi ya ce zai gama gina gidajen ne zuwa Disembar 2017. Ya kara da cewa kauyen zai hada da masallatai, makarantu, asibiti da filin wasanni.
Indimi ya ce wannan ba shi bane karo na farko da gidauniyarsa za ta yi irin haka ba kuma ba zai zama na karshe ba don a haka ma sun fara shirin gina wasu 100 a garin Ngala.
Gwamnan jihar Barno, Kashim Shettima ya ce abin da Indimi ya yi ya tabbatar da cewa shi mai kishin jihar Barno ne.
Source: Premium Hausa
Title :
Indimi Ya Gina Gidaje 100 A Bama Da Ngala
Description : Shahararren attajirin nan kuma sirikin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Muhamadu Indimi ya na gina gidaje masu dakuna uku-uku a garin Bama do...
Rating :
5