Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta soke sabon mukamin farin jakada da ta bai wa Shugaban Kasar Zimbabwe Robert Mugabe bayan ta sha matsin lamba.
"Na saurari duka korafe-korafen da jama'a suka yi cikin nutsuwa," in ji sabon Shugaban hukumar Tedros Adhanom Ghebreyesus a wata sanarwa da ya fitar.
Sai dai shugaban ya taba yaba wa Zimbabwe game da yadda take aiki tukuru a fannin kiwon lafiyar al'umma.
Sai dai wadansu masu sharhi suna ganin fannin kiwon lafiyar kasar ya tabarbare karkashin mulkin shekara 30 na Mugabe.
A ranar Juma'a ne hukumar ta nada shugaban matsayin farin jakadanta, abin da ya jawo kakkausar suka daga kungiyoyi da mutane dama a duniya.
Source: BBC Hausa
Title :
Hukumar WHO Tasoke Mukamin Da Akabawa Mugabe
Description : Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta soke sabon mukamin farin jakada da ta bai wa Shugaban Kasar Zimbabwe Robert Mugabe bayan ta sha matsin lam...
Rating :
5