A ranar Juma’a ne shugaban hukumar Hisba na jihar Kano Dahiru Muhammed ya sanar da cewa sun kama mabarata 55 daga titunan jihar.
Kamar yadda aka sani Hisba na irin haka a duk bayan dan kwanaki a titunan jihar.
A yanzu haka Muhammed ya ce suna kama wasu mabarantan wanda 17 daga cikin su yara ne sannan 38 manya.
‘‘Mun kama mabarata 33 yan asalin jihar Kano sannan 22 daga jihohin Abia,Bauchi, Jigawa da Katsina’’.
Ya ce sun kama mabaratan a titunan Bata,France Road, Hadejia Road,Kwara da Katsina Road.
Source: Premium Hausa
Title :
Hisba Takama Mabarata 55 A Titunan Jihar Kano
Description : A ranar Juma’a ne shugaban hukumar Hisba na jihar Kano Dahiru Muhammed ya sanar da cewa sun kama mabarata 55 daga titunan jihar. Kamar yadd...
Rating :
5