Wani rahoto kan cinikiyyar hauren giwa ta haramtacciyar hanya ya ce an kwato haure da dama a bara, sai dai an samu raguwa a yawan hauren giwaye da ake cirewa a duniya.
Kungiyar CITES da ke sa ido kan kasuwanci da ake yi da dabbobin da suke fuskantar barazana, ta ce an samu raguwa yawan hauren giwaye da ake cirewa a wurare da dama a Afrika.
Sai dai wakilin BBC ya ce kawo yanzu ana cigaba da kashe giwaye a nahiyar Afrika kuma ana cigaba da samun raguwa a yawan giwayen da ake da su a duniya.
Tan 40 na hauren giwa ne aka kwato a bara.
Matsalar ta ragu sosai a gabashin Afrika, wadda ta rasa rabin giwayenta a cikin shekaru goma da suka gabata.
Shugaban kungiyar ta CITES , John Scanlon ya ce shiirin kare giwaye na kasashen duniya ya soma yin tasiri, amma ya ce ana bukatar karin matakai.
Source: BBC Hausa
Title :
Haryanzu Giwayen Afirka Na Fuskantar Barazana
Description : Wani rahoto kan cinikiyyar hauren giwa ta haramtacciyar hanya ya ce an kwato haure da dama a bara, sai dai an samu raguwa a yawan hauren giw...
Rating :
5