Dan wasan gaban Tottenham, Harry Kane, ba zai buga wasan da kungiyarsa za ta yi da Manchester United ba ranar Asabar saboda raunin da ya ji a kafarsa.
Kane ya ci kwallaye biyu lokacin da Tottenham ta lallasa Liverpool da ci 4-1 ranar Lahadi, kafin a sauya shi a minti na 88.
Dan kwallon shi ne wanda ya fi kowa zura kwallo a raga a gasar firimiyar bana, inda yake da kwallo takwas.
"Likitoci ne suka bukaci dan wasan ya huta," in ji kocin Tottenham Mauricio Pochettino.
A wani sako da aka wallafa a shafin Twitter na kungiyar, ya ce "karamin rauni dan wasan ya samu a kafarsa ta dama."
Kane ya ci kwallaye 13 a wasanni 12 da ya buga wa Tottenham a kakar bana - kungiyarce take mataki na uku a gasar firimiyar bana.
Manchester United ce ta biyu a teburin, kuma makin su daya da Tottenham.
Source: BBC Hausa
Title :
Harry Kane Bazai Buga Karawarsu Da Man Utd Ba
Description : Dan wasan gaban Tottenham, Harry Kane, ba zai buga wasan da kungiyarsa za ta yi da Manchester United ba ranar Asabar saboda raunin da ya ji ...
Rating :
5