Cutar ‘Monkey Pox’ cuta ce da take kama fatar mutane inda zaka ga mai dauke da cutar na fama da wasu irin manya-manyan kuraje da ba irin na cutar kazuwa ba.
Ita dai wannan cutar ta bullo ne a jihar Bayelsa sai dai har yanzu ba a sami labarin ko wani ya rasa ransa ba a dalilin kamuwa da ga cutar.
Rahotanni ya nuna cewa namun daji kamar su birai da beraye dake shawagi agidajen mutane na daga cikin ababen dake kawo cutar ‘Monkey Pox’.
Kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta ce kwayar cutar ‘Monkey Pox’ yakan dauki tsawon kwanaki 6 zuwa 16 kafin ya fara nunawa a jikin mutum.
Alamu dake nuna an kamu;
1. Zazzabi.
2. Yawan jin gajiya a jiki.
3. Ciwon jiki musamman baya.
5. Kumburin jiki musamman idan cutar ta fara nunawa.
6. Fitowan kuraje a jikin mai dauke da cutar.
Hanyoyin da za a bi don gujewa kamuwa daga cutar;
1. A daina cin naman dabbobin daji kamar su biri, burgu da bera.
2. A hana dabbobi yawo musamman wadanda ke kiwon su domin kada su fita su dauko cutar daga jikin dabbobin da suke dauke da cutar kuma a killace dabbobin da suka kamu da cutar saboda hana yaduwar ta.
3. Mutane su nisanta kansu daga dabbobi musamman daga kashin su da kuma jikinsu.
4. Kada a zauna daki daya da mutanen da suka kamu da cutar saboda akan kamu da cutar idan wanda ke dauke da cutar ya yi tari ko kuma idan ruwan kurjin ya shafi jikin wanda bashi da cutar.
5. A yi amfani da safan hannu wajen kula da mutanen da suka kamu da cutar musamman ma’aikatan asibiti sannan idan aka ziyarci wanda ke dauke da cutar a tabbatar an wanke hannaye da ruwa da sabulu bayan an fito.
6. A tabbatar cewa a kowani lokaci ana tsaftace muhalli.
7. Sumbatar mai dauke da cutar kan iya kawo cutar.
8. A rage shan hannu ko ta yaya sannan a yi amfani da sinadarin tsaftace hannu.
Source: Premium Hausa
Title :
Hanyoyin Da Zaabi Don Kaucewa Kamuwa Da Cutar Money pox
Description : Cutar ‘Monkey Pox’ cuta ce da take kama fatar mutane inda zaka ga mai dauke da cutar na fama da wasu irin manya-manyan kuraje da ba irin na ...
Rating :
5