Gwamnan Jihar Sokoto Aminu Tambuwal, ya roki gwamnatin tarayya da ta tsame hannun ta daga kula da manyan titinan kasar nan, ta bar su a hannun jihohin da su ka ratsa.
Tambuwal ya yi wannan rokon ne a jiya Litinin a Sokoto, yayin da Kwamitin Majalisar Dattawa mai kula da manyan titinan Gwamnatin Tarayya su ka kai masa ziyara a Sokoto.
“Ina rokon Gwamnatin Tarayya ta bar manyan titina a karkashin kulawar jihohi, domin gwamnoni sun fi kusa da titinan. Don haka kasancewa sun fi gwamnatin tarayya sanin halin da titi ke ciki, za su fi saurin kai daukin gyara a duk lokacin da wani sashe na titi ya lalace.”
Da ya ke wannan jawabi, ya kuma roki kwamitin a karkashin shugaban sa Sanata Kabiru Gaya, da ya sa baki gwamnatin tarayya ta kara wa jihohi kudin kula da titina.
Sanata Gaya ya shaida wa Gwamna Tambuwal cewa sun je Sokoto ne domin yin duba-garin ayyuka. Ya kuma tabbatar wa gwamnan cewa zai isar da rokon sa.
Kwamitin ya gode wa Tambuwal a bisa ayyukan ci gaban da ya ke gudanarwa. Ya kuma kara jinjina masa a bisa kokarin sa don tabbatar da kammala gyaran titin gwamnatin tarayya da ya tashi daga Sokoto ta bi ta Jega, ta zarce Yawuri, ta mike har Kontagora.
Source: Premium Hausa
Title :
Gwamnatin Tarayya Sun Bar Jihohi Su Kula Da Manyan Titunan Kasar Nan-Tambuwal
Description : Gwamnan Jihar Sokoto Aminu Tambuwal, ya roki gwamnatin tarayya da ta tsame hannun ta daga kula da manyan titinan kasar nan, ta bar su a hann...
Rating :
5