Gwamnatin Najeriya tana son hana likitocin da ke aiki a asibitocin hukuma aiki na kashin kansu.
Ministan lafiyar Najeriya, Isaac Adewole, shi ne ya bayyana hakan da yake jawabi ga manema labarai a fadar shugaban kasar.
A cewarsa noma ne kawai sana'ar da dokar aikin gwamnatin Najeriya ta bai wa ma'aikatanta damar yi.
Saboda haka, majalisar zartawar kasar ta kafa kwamitin da za ta shawarci gwamnati game da yadda za ta yi da likitocin da ke aikin gwamnati tare da yin aikin kansu.
Baya ga haka majalisar zartarwar ta sake yanke shawarar fara hana ma'aikatanta da suka shiga yajin aiki albashi na lokacin da ba sa aiki.
Masu sharhi dai na ganin wannan mataki zai yi tasiri wajen inganta bangaren kiwon lafiya saboda yadda mafi yawan likitocin da ke aiki a asibitocin gwamnati ba sa mayar da hankali sosai kan aikinsu kamar yadda suke yi a aikinsu na kashin kansu.
Source: BBC Hausa
Title :
Gwamnati Zata Hana Likitoci Aiki Na Zaman Kansu
Description : Gwamnatin Najeriya tana son hana likitocin da ke aiki a asibitocin hukuma aiki na kashin kansu. Ministan lafiyar Najeriya, Isaac Adewole, s...
Rating :
5