Kocin Tottenham Mauricio Pochettino ya ce, maganganun da Pep Guardiola ya yi na cewa kungiyar ta dogara ne a kan Harry Kane "rainin wayo ne".
Kocin Mancherster City ya bayyana kungiyar a matsayin "kungiyar Harry Kane", yayin da yake magana a kan abokiyar hamayyarsa.
Dan kwallon ya ci kwallo 11 a wasa bakwai da kungiyar ta buga a bana.
Pochettino ya kara da cewa: "Guardiola na cikin wadanda suka kawo nasara a Barcelona kuma ban taba cewa kungiyar Lionel Messi ba ce."
A gobe Asabar ne Tottenham za ta karbi bakuncin Bournemouth a filin wasa Wembley.
Source: BBC Hausa
Title :
Guardiola Ya Raina Mana Wayo-Pochettino
Description : Kocin Tottenham Mauricio Pochettino ya ce, maganganun da Pep Guardiola ya yi na cewa kungiyar ta dogara ne a kan Harry Kane "rainin way...
Rating :
5