Kamfanin sadarwa na Google ya janye takunkumin da ya sa kan yada hoton rawar 'yan mata ba riga da ake yi a kasar Swaziland kan shafinta na wallafa bidiyo na Youtube, in ji jaridar Mail and Guardian ta Afirka Ta Kudu.
Jaridar ta Mail and Guardian ta ambato wani wakilin kamfanin Google din yana cewa sun yanke hukuncin cire takunkumin daga bidiyon ne saboda 'ba ya cikin manufarta na takaita bayyana tsiraici a irin wannan yanayin da al'ada ta amince da bayyana tsiraici".
Matakin ya zo ne a matsayin martani ga wani kamfe da Lazi Dlamini, shugaban gidan talabijin na Yabantu, da ke watsa bidiyonta a kafar Intanet kuma take shirye-shirye masu karewa da adana da kuma mayar da dabi'un Afirka.
An kirkiri shafin da ake wallafa bidiyon al'adun Afirkar ne a You Tube a shekarar 2016 - kuma yana samun masu bibiya 3,000 zuwa 4,000 a ko wanne wata har zuwa lokacin da shafin na YouTube ya fara nuna alamar cewar shirye-shiryensa ba su dace ba.
Ya kuma saka wa shafin wata alama da ke nuna wa masu talle cewar shirye-shiryensa ba su dace da yawancin muradun masu talle ba.
Mista Dlamini ya ce shi ya tuntubi Google ne domin ya bayyana cewa shi kawai yana nuna al'adun mutanensa ne, amman kamfanin ya ce shirye-shiryen na kunshe da abubuwan da suka saba wa ka'idojinta.
Sa'annan ya shirya wani jerin zanga-zanga tare da kungiyoyin al'ada sama da 200 daga Swaziland, inda aka yi zanga-zanga ta farko ranar Asabar a birnin Durban.
Zanga-zangar ta kunshi a kalla mata 12 wadanda suka tsaya da mamansu a waje dauke da kwalaye da ke cewa: "Google na nuna wariya" da kuma "(ganin) nuna nono ba rashin dacewa ba ce".
Nobukhosi Mtshali, wadda daliba ce a jami'ar Witz kuma mai fafatukar 'yancinta na bayyana al'adarta ta Swazi, tana kallon takunkumin wani hari ne kan al'adarta.
"Ni, a matsayina na 'yar Afirka Ta Kudu , ina son in yi alfahari da al'ada ta.
"In aka nuna cewa hotona bai dace ba, ko kuma na batsa ne, ina ganin wannan hari ne kai tsaye kan ala'adata. Ina ganin wannan wata alama ce ta jahilci...
"Idan ina tsayuwa ta hanyar da za ta ja hankali ne wannan wata aba ce ta daban, amman idan na wallafa hotona na cikin rigar tufafin al'adata, wannan wani abu ne daban.
Source: BBC Hausa
Title :
Goggle Ta Amince Da Yada Bidiyon Rawa Tsirara
Description : Kamfanin sadarwa na Google ya janye takunkumin da ya sa kan yada hoton rawar 'yan mata ba riga da ake yi a kasar Swaziland kan shafinta ...
Rating :
5