Gobara ta lakume wasu sassan California cikin sauri kuma ta yi sanadiyyar mutuwar mutum 10.
An ayyana dokar ta baci a wasu yankuna da ke arewaci, bayan dumbin mutane da aka kwashe da kuma asarar dukiyoyi da aka tafka.
Mutum dubu 20 ne suka tsere daga yankunan Napa, da Sonoma da kuma Yuba, a daya cikin gobara mafi ya muni da aka taba fuskanta a jihar.
An fi samun barkewar gobara a kudancin California, sai dai yanayin bazara da kuma iska mai karfi sun taimaka wajan haddasa barnar da wutar ta yi a arewaci.
Gwamnan California da ya ayyana dokar ta bacin, Jerry Brown, ya ce gobarar ta lalata ababen more rayuwa kuma tana barazana ga dubban gidaje, lamarin da ya sa aka dauki matakin kwashe mutane.
Masu hasashen yanayi a BBC sun ce babu wata alama ta samun ruwan sama a 'yan kwanaki masu zuwa, domin ma'aikatan kwana-kwana su samu damar shawo kan gobarar cikin sauki.
Haka kuma gobara ta kona gidaje 24 a kudancin California, abin da kuma ya tailastawa mazauna tsaunukan Anaheim da ke yankin Orange County barin wurin.
Shin me ne mu ka sani game da asarar rayuka da kuma ta'adin da gobarar tayi?
Kawo yanzu babu cikakken bayani game da mutuwar mutum bakwai a yankin Sonoma, sai dai shugaban 'yan sanda na yankin Rob Giordano, ya ce yana tsammanin adadin zai karu.
Ya ce akwai gidaje da kuma wurare da dama da suka kone, a kan haka za a iya samun karin mutane da suka hallaka.
Mutum biyu sun rasu a yankin Napa, yayin da mutum guda ya mutu a yankin Mendocino, inda dubban filayen gonaki suka kone.
Babu kowa a wuraren hada barasa na masu hannu da shuni .
An rufe daya daga cikinsu wanda malakar wani mawaki ne, Dave Mathews, kuma wurin na fuskantar barazana daga gobarar a cewar wani ma'aikacin kamfanin.
Babu cikakken bayani kan yadda wutar ta tashi a daren Lahadi, amma gobarar na ci cikin sauri saboda mastananciyyar iska da kuma zafi da ake fuskanta.
Mazauna yankin da suka bar gidajensu na samun mafaka a matsugunai daban-daban.
Gobarar ta zo ne a wani yanayi na zafi da ba a taba ganin irinsa ba da kuma fari, a cewar jaridar San Francisco Chronicle.
Source: BBC Hausa
Title :
Gobara Ta Lashe Guraren Hada Barasa A San Fransisco Na America
Description : Gobara ta lakume wasu sassan California cikin sauri kuma ta yi sanadiyyar mutuwar mutum 10. An ayyana dokar ta baci a wasu yankuna da ke ar...
Rating :
5