Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta ce tana duba yiwuwar kirkiro sabbin mazabu a gidajen yari da ke kasar.
Shugaban hukumar zaben Farfesa Mahmood Yakubu ya shaida wa wasu kungiyoyin farar hula a Abuja cewa, akwai wasu rukunoni na 'yan fursuna da za'a ba su damar kada kuri'a a zaben 2019.
Sai dai Farfesa Yakubu bai bayyana rukunonin fursunonin ba.
Akwai fiye da fursunoni dubu 68,000 da ake tsare da su a gidajen yari daban-dabam a fadin kasar.
Galibin fursunonin dai suna jira ne a yi musu shari'a.
Kungiyoyi da sauran masu fafutika a Najeriya sun dade suna matsin lamba ga hukumomi don su ba 'yan fursuna damar kada kuri'a.
A cewar kungiyoyin, rashin bai wa fursunoni damar yin zabe tamkar tauye hakkokinsu ne.
A watan Fabrairun 2019 ne za a gudanar da babban zabe a Najeriya.
Source: BBC Hausa
Title :
Fursunoni Zasuyi Zabe 2019
Description : Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta ce tana duba yiwuwar kirkiro sabbin mazabu a gidajen yari da ke kasar. Shugaban hukumar zab...
Rating :
5