Hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa, ta wanke Juventus kan cinikin Paul Pogba da ta sayar wa Manchester United kan kudi fam miliyan 89.3 a bara.
Tun a watan Yuni Fifa ta ce United ba ta laifi kan sayan dan kwallon da ta yi, amma ta zargi Juventus da laifin hada baki da wakilin Pogba, Mino Railo wajen karya ka'idar hukumar.
Amma yanzu hukumar ta ce babu wani hukuncin da za ta dauka kan Juventus bayan da kwamitin ladabtarwa ya kammala bincikensa, bai kuma sameta da laifi ba.
Kwamitin ya ce bai samu kwakkwarar shaida cewar kungiyar ta karya dokar cinikin Pogba da ta yi zuwa United ba.
Source: BBC Hausa
Title :
Fifa Ta Wanke Juventus Kan Batun Pogba
Description : Hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa, ta wanke Juventus kan cinikin Paul Pogba da ta sayar wa Manchester United kan kudi fam miliyan 89.3 a b...
Rating :
5