Kungiyoyin Hamas da Fatah sun sanya hannu kan yarjejeniyar sasanta tsakaninsu a birnin Alkhahira na kasar Masar, a wani yunkuri na kawo karshen barakar da ke tsakaninsu.
Masar, wadda ta karbi bakuncin tattaunawar, ta ce hukumomin Falasdinawa da ke samun goyan bayan Fatah, za su karbe dukkanin aikace-aikacen gudanarwa a zirin Gaza daga hannun kungiyar Hamas, kama daga ranar 1 ga watan Disamba.
Har ila yau za a mika mashigar Rafa daga Gaza zuwa Masar nan ba da jimawa ba ga ikon wata gwamnatin hadin-kai.
Kasar Masar ce ta jagoranci tattaunawar sulhu tsakanin kungiyoyin biyu a birnin Alkhahira, inda yanzu kuma kungiyar Falasdinawa ta Hamas ke cewa ta cimma yarjejeniyar sulhu da abokiyar hamayyarta wato Fatah, domin kawo karshen sabanin da ke tsakaninsu a tsawon fiye da shekara 10.
Shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas, ya ce wannan yerjejeniyar ita ce tattaunawar zaman lafiya ta karshe tsakanin kungiyoyi biyun da basa ga-majici-da-juna.
A watan da ya gabata ne dai kungiyar Hamas ta ce ta soke kwamitin da ke gudanar da yankin Gaza tare da mika ikon yankin ga gwmanatin Fata a gabar yammacin kogin Jordan.
Kungiyar Hamas dai ta karbe ikon yankin Gaza ne, yayin da takwararta ta Fatah take iko da gabar Yammacin Kogin Jordan bayan mummunan fadan da suka yi a shekarar 2007.
Rikicin ya barke ne bayan Hamas ta samu nasarar lashe zabe.
Zakaria al-Agha wani babban jami'in kungiyar Fatan ne, a yankin zirin Gaza ya kuma tabbatar da cewa an kulla yarjejeniyar.
Ya ce: "Mun cimma yarjejeniyar danganen da duka abubuwan da muka tattauna a kansu a wannan tattaunawar da aka yi a a kasar Masar yau da safe."
Ya ci gaba da cewa: "Kuma mun cimma matsaya akan ilahirin bambance-bambancen da ke tsakaninmu."
Mista Al-Agha ya ce yana fatan Shugaban Falasdinwa Mahmoud Abbas zai ziyarci yankin Gaza a cikin wannan watan, bayan shafe shekera goma ba tare da ziyartar yankin ba.
Ya ce: "Ina fatan idan Allah Ya yarda a samu yin wata tattaunawa da za ta hada shugabanin duka bangarorin biyu a kasar Masar, zuwa karshen watan nan, bayan haka kuma da yardar Allah a cikin wannan watan Mahmud Abas ya ziyarci yankin zirin Gaza."
An dai raba Falasdinawan da ke zaune a zirin Gaza da wadanda ke zauni a gabar yamma da Kogin Jordan da juna ne tun lokacin da rikici ya barke tsakanin kungiyoyin biyu a shekarar 2007 wanda kuma ya haddasa asarar rayuka.
Tun shekarar 2006 ne dai kasar Masar da Isra'ila suka rufe kan iyakokinsu da yankin na Gaza.
Isra'ila dai na matukar adawa da shigar kungiyar Hamas cikin gwamnatin Falasdinawa.
Tana mai daukar kungiyar ta Hamas a matsayin kungiyar 'yan ta'adda, inda ta ce ba za ta tattauna da gwamnatin Falasdinawa wacce ke kunshe da 'yan Hamas a cikinta.
Mazauna zirin Gazan dai na fatan yarjejeniyar za ta saukaka harkokin kan iyaka tare da kawo habakar tattalin arziki.
Source: BBC Hausa
Title :
Falasdinawa Sun Sasanta Junan Su
Description : Kungiyoyin Hamas da Fatah sun sanya hannu kan yarjejeniyar sasanta tsakaninsu a birnin Alkhahira na kasar Masar, a wani yunkuri na kawo kars...
Rating :
5