Kungiyar kwallon kafa ta Everton ta sallami kocinta Ronald Koeman, bayan da ya yi rashin nasara da ci 5-2 a hannun Arsenal a ranar Lahadi a gasar Premier.
Doke Everton da Arsenal ta yi ya sa kungiyar ta koma kasan teburi ta 18, bayan da ta ci wasa biyu a karawa tara da ta yi a gasar ta Premier.
Koeman mai shekara 54 ya ja ragamar Everton ta kare a matsayi na bakwai a gasar Premier ta bara, kuma a bana ya kashe fam miliyan 140 wajen sayo sabbin 'yan kwallo.
Koeman ya zama koci na uku da aka sallama daga aiki a gasar Premier a bana, bayan Frank de Boer da Crystal Palace ta kora da Craig Shakespeare wanda ya raba gari da Leicester City.
Source: BBC Hausa
Title :
Everton Ta Kori Kocinta
Description : Kungiyar kwallon kafa ta Everton ta sallami kocinta Ronald Koeman, bayan da ya yi rashin nasara da ci 5-2 a hannun Arsenal a ranar Lahadi a ...
Rating :
5