Jami'an lafiya daga sassan duniya daban-daban na gudanar da wani taro ranar Laraba a Faransa don daukar gabara kan takaita yawan mace-macen da ake samu sakamakon annobar cutar kwalara da kashi 90 cikin 100 kafin nan da shekara ta 2030.
Wannan shi ne karon farko da aka taba daukar irin wannan alkwarin.
Taron na zuwa ne lokacin da Yemen ke tunkarar annobar amai da gudawa mafi muni a tarihi, yayin da kungiyoyin agaji kuma ke gargadi game da barkewar cutukan da ake samu daga ruwa a Bangladesh.
Ana sa rai taron zai hada fuskokin jami'an gwamnatoci da na Hukumar Lafiya Ta Duniya da hukumomin ba da agaji da masu ba da gudunmawa a karon farko inda za su dauki alkawarin tunkarar cutar amai da gudawa.
Cutar kwalara na janyo mutuwar mutane kimanin 100, 000 duk shekara a sassa daban-daban na duniya, amma dai ta fi kamari a kasashen Afirka da Asiya,
Tim Wainwright, babban jami'i ne na kungiyar Wateraid mai rajin samar da tsaftataccen ruwa a duniya ya ce, ta hanyar samar da ruwa da tsaftar muhalli da ta jiki ga daukacin al'ummar duniya, ana iya shawo kan cutar kwalara.
"Wannan cuta ce ta cikin karni na 19. An gano ta kuma an kakkabe ta shekara 150 da ta wuce a London da New York.
Abin kunya ne a ce har yanzu duniya na fama da kwalara, dalilin kuma da ke janyo haka shi ne rashin ruwa da rashin amintattun bandakuna da ingantacciyar tsafta.
Mutane sama da miliyan dubu 2 ne a fadin duniya ba su da bandaki mai aminci".
Shi ma wani kwararre kan cutar amai da gudawa a Hukumar Lafiya Ta Duniya, Dr. Dominique Legros ya ce taron Faransa na kira ne da a yunkura ta hanyar tunkarar kwalara kafin ta barke.
"Takaita barkewar cutar amai da gudawa wani abu ne mai matukar sauki. Cuta ce wadda ba cikin sauri take yaduwa ba kuma tana bukatar ruwan da ya gurbata sosai.
To samar da tsaftataccen ruwa kadai ya isa, ba batu ne mai sarkakiya ba. Magana ce ta samo abokan kawance da kasashe da kuma masu ba da gudunmawa don su zuba jari a wannan bangare.
Amma kamar yadda aka sani inda ake samun barkewar cutar kwalara, wurare ne mafi talauci a duniya. Wannan cuta ce da aka yi biris da ita kuma take auka wa mutanen da aka yi biris da su."
Kwararrun sun ce akwai bukatar a samar da allurar rigafin cutar domin dakile barkewarta.
Source: BBC Hausa
Title :
Duniya Na Taro Kan Cutar Kwalara
Description : Jami'an lafiya daga sassan duniya daban-daban na gudanar da wani taro ranar Laraba a Faransa don daukar gabara kan takaita yawan mace-ma...
Rating :
5