Kotun Koli a Kasar India ta soke dokar da zai ba namiji da mace a gidan aurensu damar saduwa da juna kafin su kai shekara 18.
Akwai dokar Kasar ‘Penal Code’ da ya amince wa mace da namiji ‘yan kasa da shekara 18 suyi aure sannan kuma za su iya saduwa da juna a wannan lokaci. Kamar daga shekara 15 – 17.
Wannan doka da ake amfani da shi dai yanzu zai zama laifi a kasar bayan soke shi da kotun kolin tayi.
Kotun tace duk wanda yayi aure bai kai shekaru 18 ba bazai sadu da matar sa ba sai har ya kai wadannan shekaru. Yin haka a sabuwar dokar aikata fyade ne.
” Ita matar za ta iya kai kara idan har mijinta ya nemi saduwa da ita a wannan lokaci da bata kai shekara 18 ba.”
Source: Premium Hausa
Title :
Duk Wanda Ya Sadu Da Macen Dabata Kai Shekara 18 Ba Ya Aikata Fyade
Description : Kotun Koli a Kasar India ta soke dokar da zai ba namiji da mace a gidan aurensu damar saduwa da juna kafin su kai shekara 18. Akwai dokar K...
Rating :
5